✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun cafke kasurguman barayin shanu a Zamfara

Daya daga cikin barayin ya bayyana yadda suke daukar hayar bindigogi.

Rundunar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta cafke wasu kasurguman barayin shanu guda biyu a Jihar Zamfara.

Kakakin NSCDC na Jihar Zamfara, Oche Ikor, ya shaida wa manema labarai a Gusau cewa an damke barayin shanun ne a tashar mota.

Mista Ikor ya ce rundunar ta cafke su a tashar mota ne a yayin da suke kokarin yin tafiya zuwa Jihar Taraba a ranar Litinin.

Daya daga cikin barayin da suka shiga hannu ya shaida wa jami’an tsaro cewa bai san iya adadin satar shanun da ya yi ba, sannan ya kashe mutum shida.

Barawon shanun da ya ce ya fito ne daga kauyen Agama Lafiya da ke Karamar Hukumar Gusau, ya bayyana cewa sukan hadu ne a garin Gusami na Karamar Hukumar Birnin Magaji na jihar kafin fita yin satar shanu.

“Muna daukar hayar bindigogi da muke kashe mutane kuma ina tabbatar maka da cewa mun kai hare-hare wurare da dama kuma ana biyan mu N10,000 a kan duk harin da muka kai.

“Ba ni da bindiga, ban san a ina shugabanninmu ke samo su ba, amma a lokuta da dama ana sa ni raba shanu a cikin daji, wannan shi ne abin da na kware wajen yi,” a cewarsa.

Kakakin rundunar ya ce tuni aka shiga gudanar da bincike domin kama abokan aikin nasu.