✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun cafke masu garkuwa da mutane 4 a Edo

An yi nasarar ceto wasu mutum biyar yayin samamen da jami'an tsaron suka kai a wani daji

Rundunar hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji da ’yan banga sun cafke mutum hudu masu garkuwa da mutane, tare da ceto wasu mutum hudu a hannunsu a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.

Dubun ’yan bindigar ta cika ne a yayin da jami’an tsaron suka kai samame dajin Era da ke yankin Ekpoma a Karamar Hukumar Esan ta Yamma.

Kakakin ’yan sandan jihar, Bello Kontongs, ya ce an cafke mutum hudun ne a wurare daban-daban a cikin dajin.

Kontongs ya ce daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, akwai mutum biyu da aka biya Naira miliyan 2.4 kudin fansarsu, amma ’yan bindigar suka ki sakin su.

Ya kara da cewa mutanen da aka sace din, an yi garkuwa da su ne a ranar 1 ga watan Disamba 2021.

Ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar ce bayan samun bayanan sirri cewa an hangi wasu mutum 20 a cikin wata mota kirar bas.

Bayan samun rahoton ne aka yo hadin gwiwar jami’an tsaron da suka yi tseratar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Kakakin ’yan sandan ya ba wa jama’ar jihar tabbacin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu, tare da bankado masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar.