✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun ceto karin fasinjar jirgin kasan Edo

Adadin wadanda aka ceto ya kai mutum bakwai kawo yanzu.

Hadin gwiwar jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda, ’yan banga da mafarauta sun sake ceto wata mace daga cikin fasinjojin jirgin kasan Edo da ’yan bindiga suka sace.

An ceto ne a ranar Talata, wanda hakan ya kara adadin wadanda aka ceto zuwa mutum bakwai.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwanbuzor, ya tabbatar da adadin wadanda aka ceto zuwa mutum bakwai.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga suka kai hari tashar jirgin kasa ta Igueben da ke Jihar Edo, a ranar Asabar, suka yi awon gaba da fasinjoji 32.

Bayan sace fasinjojin ’yan bindigar sun nemi iyalansu su biya diyyar Naira miliyan 20 kan kowane mutum daya.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka taba kai wa hari tare da sace fasinjojin jirgin kasa a Najeriya.