✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun ceto mutane 4, sun cafke ‘yan bindiga 3 a Kaduna

Bayan ceto mutane hudu da jami'an tsaro suka yi, sun yi nasarar cafke 'yan bindiga uku.

Rundunar tsaro ta ‘Operation Thunder Strike’ ta ceto mata biyu da aka yi garkuwa da su a Gadanin Gwari dake yankin Gwagwada a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Asabar.

A cewar sanarwar, “Sojoji sun yi nasarar yin artabu da ‘yan bindiga har suka ci karfinsu, wasu kuma suka gudu.

“Uku daga cikin ‘yan bindigar sun shiga hannu, an tseratar da mata biyu da suka yi garkuwa da su,” cewar Aruwan.

Kwamishinan ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da matan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.

Kazalika, ‘yan sandan jihar Kaduna sun ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kurmin Idon, dake kan titin Kaduna zuwa Kachia a karamar hukumar Kajuru.

Aruwan ya kara da cewa tuni rundunar tsaron ta ci gaba sintiri a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, ya jinjinawa sojojin da ‘yan sandan jihar kan yadda suka ceto mutanen da aka yi garkuwar da su.