✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindigar da suka kai hari kauyen Zamfara

’Yan ta’addan dai sun sha yunkurin kai wa garin na Magami, amma ba sa samun nasara.

Jami’an tsaro tare da gudunmawar ’yan sa-kai a ranar Lahadi sun fatattaki ’yan bindigar da suka kai hari kauyen Magami da ke Karamar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.

Aminiya ta gano cewa gungun maharan da ke kan babura dai sun yi yunkurin kai hari yankin da rana, amma suka hadu da tirjiya daga jami’an tsaron.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa a matsayin Babangida, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Sun firgita jama’a da dama, yayin da mazauna yankin suka fara gudun neman tsira da rayuwarsu. ’Yan kasuwa sun rika rufe shagunansu suna tafiya gida.

“Maharan sun zo ne a kan babura sannan suka hadu a kusa da Sabon Garin Dutsen Kura, mai nisan kilomita 15 daga garin Magami.

“Da mutanen yankin suka ga alamun harin, sai suka ankarar da jami’an tsaro da suke garin na Magami, wadanda su kuma tare da ’yan sa-kai suka yi musu kwanton-bauna a Filin Idi na garin.

“Suna zuwa, ala tilas suka yi saduda suka juya,” inji Babangida.

’Yan ta’addan dai sun sha yunkurin kai wa garin na Magami hari a baya-bayan nan, amma ba sa samun nasara.

Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.