✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun hallaka kwamandan kungiyar IPOB

‘Ikonso Commander’ da yaransa sun sheka barzahu a maboyarsu da ke Jihar Imo.

Jami’an tsaro sun bindige kwamandan haramtacciyar kungiyar IPOB, mai neman ballewa daga Najeriya wanda ya jagoranci harin da aka kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Imo.

A safiyar Asabar, jami’an tsaron hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da DSS suka hallaka ‘Ikonso Commander’ da yaransa shida suka kuma cafke wasu a maboyarsu da ke kauyen Oromama da ke Karamar Hukumar Oru ta Gabas a Jihar.

Jami’an tsaron sun kuma kwato tarin makamai a samamen da suka kai bayan da ’yan bindiga suka kai hari a gidan Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma, suka kashe jami’an tsaro.

Wani babban jami’i a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa ya ce a yayin bin sawun maharan ne jami’an tsaron suka kai samamen a maboyar IPOB da ke kauyen.

“Jami’an tsaron na tunkarar wurin sai ’yan kungiyar suka bude musu wuta babu kakkautawa; Su kuma nan take suka mayar da martani.

“Sun kashe babban kwamandan ’yan tawayen na yankin Kudu maso Gabas wanda ake wa lakabi da ‘Ikonso Commander’ da wasu mayakan kungiyar guda shida.

“Ikonso shi ne mataimaki kuma mai shirya hare-haren da kungiyar take kaiwa a wurare daban-daban.

“Shi ne ya kitsa ya kuma jagoranci harin da aka kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Imo da wasu hare-haren da aka kai wa jami’an tsaro da sansanoninsu,” inji majiyar.