✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 10 a Kaduna

An kone sansaninsu da wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.

Jami’an tsaron sun kashe ’yan bindiga 10 a yankin Kwanar Bataru da ke kusa da garin Fatika a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun ji jiki yayin musayar wuta da jami’ar tsaro, inda aka kone sansaninsu da sauran wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Aruwan y ace jami’an tsaron sun samu nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da ’yan bindigar suka yi garkuwa da shi.

Ya kara da cewa, ’yan bindigar da suka tsere sun bar babura da wata babbar bindiga da wayoyin salula da fitilu da kuma layu.

Kazalika, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba wa jami’an tsaron kan wannan bajinta da suka yi, inda kuma ya yi musu fatan samun karin nasara a ayyukan da ake gudanarwa na magance matsalar tsaro a fadin jihar.