✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 5, sun cafke 15 a Taraba

Jami’an tsaron sun yi nasarar hallaka ’yan ta’addan da suka addabi wasu yankunan jihar.

Hadin guiwar sojoji da ’yan sanda sun hallaka wasu ’yan bindiga biyar da suka addabi Jihar Taraba.

Rundunar ta kuma cafke ’yan bindiga 15 a wani samame da ta kai tare da ’yan banga a maboyar ’yan bindiga a dazuka da tsaunikan Kananan Hukumomin Sardaauna da Bali da Gassol na jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kashe ’yan bindigar tare da kame wasu 15 a jihar.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga sun addabi mazauna wasu yankunan jihar inda suka sace jama’a masu yawan gaske tare da karbar miliyoyi Naira a matsayin kudin fansa.

’Yan bindigar sun kuma kashe wasu daga cikin wadanda suka sace bayan sun karbi kudaden fansa.

Yawan ta’asar da ’yan ta’addan ke tafkawa ne ya sa hukumomin tsaro suka kaddamar ta farmakin, in ji majiyar.