Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda sama da 200 a Neja | Aminiya

Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda sama da 200 a Neja

    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Akote, Minna

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da ’yan ta’adda 200 sun rasa rayukansu a sakamakon luguden wuta ta tsawon kwanaki hudu da jami’an tsaro suka yi musu a Jihar Neja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an tsaron da suka hada da sojoji, ’yan sanda, Civil Defence da ’yan sa-kai sun hallaka ’yan ta’addan ne a Kananan Hukumomin Rafi, Mariga da Kontagora na jihar.

Kwamishinan Kananan Hukumomi, Harkokin Masarautu da Tsaron Cikin gida, Emmanuel Umar, ne ya tabbatar da hakan a wani taro kan lamarin tsaron jihar, yana mai cewa kungiyoyin ’yan bindiga hudu ne suke cin karensu babu babbaka a jihar.

Kwamishinan ya ce yan ta’adda da dama sun tsere da raunuka na harsashin bindiga, inda ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri wanda hakan zai bai wa hukumomi damar samun nasarar magance matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana kungiyoyin yan ta’addan hudu da suka addabi jihar sun hada da wadanda ke karkashin jagorancin Bello Turji, Yellow Janbros, Kachalla Halilu da Ali Kawaje.

Kwamishinan ya ce sun kwato babura da dobbobi da dama, kari a kan bindigogi daga hannun yan ta’addan.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta dauki azamar sauya dabarun tunkarar ’yan ta’adda kuma ta shirya kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi jihar.