✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kashe ’yan tawaye 38 a Afganistan 

Jami'an tsaron sun kashe manyan dakarun 'yan tawayen biyu a yayin samamen.

Jami’an tsaro sun kashe ’yan tawaye 38 tare da kame wasu 78 a wani samame a yankin Badakhshan da ke Arewacin kasar Afganistan.

Shugaban Sashen Yada Labarai da Al’adu na Lardin Qari, Maazudin Ahmadi ne, ya bayyana haka a ranar Litinin.

Ahmadi ya shaida wa manema labarai cewa, “A yayin da ake gudanar da aikin tsaftace muhalli a yankunan Shiwa, Arghanj Khwa da Ragh cikin mako guda da ya gabata, an kashe ’yan tawaye 38 da ke dauke da makamai tare da cafke wasu 78.”

Jami’in ya kara da cewa an kashe jami’an tsaro uku tare da raunata wasu biyar a samamen.

A halin da ake ciki, kamfanin dillancin labarai na Bakhtar ya rawaito cewa, kwamandojin ’yan tawayen biyu, wato Bahrudin da Abdul Hamid, na daga cikin wadanda aka kashe a samamen na mako guda.