✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun ragargaji IPOB a Ebonyi da Enugu

An kwace makamai da dama daga hannun 'yan bindigar da suka hada bindigogi da alburusai da babura da kayan sojoji da sauransu.

Rundunar hadin gwiwar jami’an tsaro ta Operation Golden Dawn II ta kai samame a wani sansanin IPOB/ESN a kauyen Amagu da ke Karamar Hukumar Ishielu, Jihar Ebonyi.

Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun yi dauki-ba-dadi tare da kashe wasu daga cikin mamabobin haramtacciyar kungiyar, sauran kuma suka ranta a na-kare.

A samamen na ranar Litinin, an kwace makamai da dama da suka hada da bindigogi da alburusai da babura da rigunan sojoji da sauransu.

Kazalika, jami’an tsaro sun kai makamancin samamen a wata maboyar bata-garin da ke Agubeji a Jihar Enugu inda suka cafke wani da ake zargi yana taimaka wa IPOB/ESN.

Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Brigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce wanda aka damken na ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro wajen aikinsu a yankin.

Rundunar hadin gwiwar da ta kai samamen ta kunshi sojoji da ’yan sanda da sojojin sama da kuma jami’an DSS.