✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar ABU za ta inganta noma domin bunkasa kudin shigarta

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabir Bala ya ce jami’ar za ta yi amfani da ayyukan binciken aikin gona domin ta bunkasa…

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabir Bala ya ce jami’ar za ta yi amfani da ayyukan binciken aikin gona domin ta bunkasa samar da kudin shigarta da sauran ayyukan bincike.

Farfesa Bala ya bayyana hakan lokacin bikin nuna aikace-aikacen da cibiyar binciken aikin gona ta jami’ar ke gudanarwa duk shekara a Zariya.

Ya bayyana cewa idan har jami’ar tana bukatar tsayawa da kafafunta akwai bukatar ta rinka samun kudin shiga kasancewar kudin da gwamnati ke bai wa jami’o’i domin gudanar da ayyukansu ba mai yawa ba ne kasancewar babu isassun kudi a asusun gwamnatin.

Ya ce idan aka hada aikace-aikacen da ke cibiyar da na sauran cibiyoyin binciken aikin gona na jami’ar za a sami ci gaba mai yawa da zai taimaka wa jami’ar da ma kasa baki daya.

Shugaban jami’ar ya ce abin da ya gani a wurin bukin ya nuna cewa za a iya yin amfani da ayyukan domin ciyar da jami’ar gaba.

Ya ce sashin binciken aikin gona na jami’ar Ahmadu Bello na da ingantattun aikace-aikacen bincike da ma’aikata da za su taimaka wajen samar wa jami’ar kudin shiga.

Da yake jawabi tun da farko, shugaban hukumar gudanarwa na majalisar cibiyoyin binciken aikin gona na kasa, Mista Tunji Ajegbe ya ce irin ayyuakan bincike da cibiyar ta gudanar irinsu ne kasar nan ke bukata domin ciyar da bangaren aikin gona gaba.

A don haka ya bukaci cibiyar da ta kara matsa kaimi wajen ci gaba da gudanar da bincike da kuma samar da hanyoyin da binciken zai kai ga manoma.