Jami’ar ABU Zariya ta sanar da ranar komawar dalibai | Aminiya

Jami’ar ABU Zariya ta sanar da ranar komawar dalibai

Jami’ar Ahmadu Bello
Jami’ar Ahmadu Bello

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ta sanar da ranar 25 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar komawar dalibai domin ci gaba da zangon karatu na 2019/2020.

Jami’in hulda da al’umma na jami’ar, Awwal Umar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron Majalisar Gudanarwar Jami’ar karo na 501 da aka gudanar a ranar Talata.

Mista Umar ya ce komawar daliban wajen ci gaba da daukan darussa za ta kasance rukuni-rukuni, inda daliban da ke shekararsu ta karshe za su fada rukunin farko na wadanda za su koma.

Ya ce, “Daliban aji daya da na biyu da daliban da ke karatu a fannin nazarin kiwon lafiya, za su fada a rukunin farko na masu komawa.”

“Daliban da ke karatun gaba da digiri na farko za su rika daukan darussa ne daga gida ta hanyar yanar gizo,” inji shi.

Sanarwar da Mista Umar ya fitar ta ce ragowar daliban za su kasance a rukuni na biyo kamar yadda tsarin taswirar zangon karatu na 2019/2020 ta jami’ar da aka yi wa kwaskwarima ta zayyana.

Sai dai ya ce ranar 25 ga watan Janairun da aka sanar a matsayin ranar komawar daliban na iya sauyawa gwargwadon hali na wani umarni da ka iya fita a kowane lokaci daga bakin Gwamnatin Tarayya ko kuma Gwamnatin Jihar Kaduna.

Ya ce jami’ar za ta yi amfani da abin da take da shi a hannu wajen taimakawa sashin kiwon lafiya na jami’ar waje tanadar kayayyakin kariya domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Kazalika, ya ce za a samar da wajen killace duk wasu marasa lafiyar da ta danganci annobar