✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Bayero Kano ta ce za a kammala zangon karatun 2019/2020

Jami'ar ta soke zangon ne sakamakon lalacewar jadawalin karatu da yajin aiki ya haifar.

Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da cewa za ta kammala zangon karatu na 2019/2020.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Magatakardar Jami’ar Fatima Binta Mohammed ta sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce ranar 18 ga Janairu 2021, ita ce ranar da za a fara kashin farko na zangon karatun 2020/2021.

Sannan kashi na biyu na zangon karatun zai fara ranar 3 ga watan Mayu, 2021.

Su kuwa masu karatun gaba da digirin farko, za su fara karatu ne a ranar 18 ga watan Janairu 2021, a matsayin kashin farko na zangon karatunsu a bana.

Sai kashi na biyu na zangon karatun na su zai fara ranar 1 ga Yuni, 2021.

Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta umarci daliban gaba da digirin farko da ba su yi rajista a kan lokaci ba a baya, da su yi kafin lokaci ya kure musu.

Kazalika, Majalisar Gudanarwar Jam’iar ta sauya wa zangon karatun 2019/2020 zuwa 2020/2021.

Idan ba a manta ba kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 23 ga Maris, 2020, sannan ta janye yajin aikin a ranar 22 ga Disambar 2020.

Yajin aikin da ya dauki tsawon watanni tara, lamarin da ya janyo tangarda a jadawalin tsarin karatun jami’o’in kasar nan kuma haka ya sanya Jami’ar ta yanke hukuncin soke zangon karatun tare da fara sabo.