✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Bayero ta wajabta amfani da takunkumin rufe fuska

Hukumar Jami'ar BUK ta wajabta amfani da takunkumin rufe fuska a harabarta

Hukumar Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da wajabta amfani da takunkumin rufe fuska a harabarta ga dukkan ma’aikata, dalibai da masu ziyara daga ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021.

Matakin, a cewar Jami’ar, an dauke shi ne domin takaita yaduwar cutar COVID-19, a daidai lokacin da aka sake bude makarantar bayan sama da wata 10 tana rufe saboda cutar da kuma yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU).

Sakataren Sashen Watsa Labarai na Jami’ar, Lamara Garba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

“Saboda haka, malamai, ma’aikata, dalibai, mazauna harabar makaranta da masu kawo ziyara dole ne su kiyaye da wannan umarnin.

“Tuni makarantarmu ta samar da isassun kayayyakin wanke hannu a muhimman wurare a dakunan kwanan dalibai, azuzuwa, da wuraren taruka.

“Ba dalibin da za a bari ya shiga aji ko kuma kowanne wuri a cikin jami’ar ba tare da ya sa takunkumin da ya rufe baki da hancinsa ba.

“Mun girke ma’aikata na musamman domin sa ido da kuma tabbatar da an bi matakan kariya daga cutar,” inji shi.

Jami’ar ta ce za ta hukunta duk wanda aka kama yana karya dokar.

Sanarwar ta kuma shawarci jama’a da su rage yawan gaisawa da hannu, su bayar da tazarar akalla mita biyu sannan kuma su ci gaba da wanke hannunsu a-kai-a-kai.