Jami’ar Bayero za ta fara horaswa kan shugabanci da ci gaban siyasa | Aminiya

Jami’ar Bayero za ta fara horaswa kan shugabanci da ci gaban siyasa

    Abdullahi Abubakar Umar

Jami’ar Bayero ta Kano a karkashin Cibiyar Nazarin Dimokradiyya ta Aminu Kano za ta fara bayar da horo kan Shugabanci da Cigaban Mulkin Dimokradiyya.

Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa shirye-shiryen sun yi nisa a  cibiyar da ke Gidan Mambayya a garin  Kano domin fara shiyar bayar da horon.

Ya yi wannan bayyanin ne a taron bikin cikar shekara 21 da Kafuwar cibiyar kamar yadda kafar yada labarai ta Kano Focus ta wallafa.

Ya kara bayyana cewa shirin zai mai da hankali ne kan yadda ake gudanar da harkokin jam’iyyun siyasa, gudanar da zabe, da kuma yadda aka tsarin dokoki a majalisa.

Har ila yau horon zai bunkasa kwarewa da basirar shugabannin siyasar Najeriya da masu rike da mukaman gwamnati da shugabannin jam’iyyun siyasa da dai sauransu.

An dai kafa Cibiyar Nazarin Dimokaradiyya ta Aminu Kano da ke Gidan Mambayya a Kano ne a watan Nuwamba shekara ta 2000 a matsayin sashin bincike da horaswa na Jami’ar Bayero ta Kano, a harabar da rusasshiyar Cibiyar Nazarin Dimokaradiyya (CDS), wacce Gwamnatin Tarayya ta kafa 1989.