✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Benin za ta fara bincike kan sarrafa makamin Nukiliya a Najeriya

Cibiyar dai ita ce kan gaba a fasahar a duniya

Jami’ar Benin ta ce za ta hada gwiwa da Cibiyar Binciken Makamin Nukiliya ta Turai (CERN) domin fara bincike a fannin kimiyya da fasahar Nukiliyar a Najeriya.

Sashen yada labarai na jami’ar  ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce wasu daliban makarantar su biyu, Decent Oghifo da David Dosu da a kwanakin baya suka sami nasarar tsallake tantancewar da cibiyar ta CERN za su je hedkwatarta da ke Geneva domin daukar wani kwas da ta shirya.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, wannan ne karo na farko da dalibai daga yankin Kudu da hamadar Sahara suka sami matsuguni a shirin.

Jami’ar ta kuma ce Daraktan sashen bincike da Ci gaban Jami’ar, Farfesa Musibau Bamikole, ya gabatar da daliban ga Shugaban Jami’ar Farfesa Lilian Salami, da kuma sauran shugabnnin gudanarwarta.

A nasa bangaren, Shugaban jami’ar ya bayyana farin cikinsa kan wannan nasara da daliban da ma jami’ar suka samu, tare da ayyana hadin guiwar jami’ar da cibiyar CERN a matsayin babban ci gaba da zai sake daga darajar jami’ar a Najeriya da idon duniya.