✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar FUTA ta sanar da ranar komawa makaranta

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Akure (FUTA), ta sanar da ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021, a matsayin ranar komawa…

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Akure (FUTA), ta sanar da ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2021, a matsayin ranar komawa makaranta don ci gaba da karatu kamar yadda aka saba. 

Mataimakin Daraktan Harkokin Sadarwa na Jami’ar, Adegbenro Adebanjo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Sai dai sanarwar ta gargadi daliban a kan kada su kuskura su koma makarantar gabanin wannan ranar da aka ayyana a matsayin ranar komawa.

Adebanjo ya bayyana cewa, “Duba da yanayin da ake ciki na annobar COVID-19, hukumar Jami’ar ta bukaci dukkan dalibai da su kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar kamar yadda mahukunta na lafiya suka shar’anta yayin kasancewarsu a makarantar.”

“Sanarwar ta kuma jaddadawa daliban da su tabbatar sun kasance sun sanya takunkumin rufe fuska a ciki da kewayen makarantar kuma wajibi ne su kiyaye dokar bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna.”

“Jami’ar za ta samar da sinadarin wanke hannu da wuraren wanke hannu a dukkan wuraren da suka kamata, an kuma bukaci dalibai su rika zuwa da nasu sunadarin tsaftacce hannu,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.