✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata jami’ar Musulunci na bin Ganduje bashin kudi

Jami’ar Musulunci ta  Crescent University da ke Abeokuta a Jihar Ogun ta bukaci Gwamnatin Kano ta biya bashin kudin karatun dalibai ‘yan asalin jihar da…

Jami’ar Musulunci ta  Crescent University da ke Abeokuta a Jihar Ogun ta bukaci Gwamnatin Kano ta biya bashin kudin karatun dalibai ‘yan asalin jihar da suka kammala karatunsu a jami’ar.

A wata wasika da wanda ya asassa jami’ar Bola Ajibola ya aike wa gwamnatin jihar Kano, ya bukaci gwamnatin da ta yi wa Allah ta biya ta bashin kudin karatun daliban da ta dauki nauyi.

Bola Ajibola ya ce bashin ya kai Naira miliyan 55 da dubu 28 da da naira 250 da makarantar ke bin jihar a matsayin ragowar kudin karatun daliban.

Ya ce jami’ar ta bai wa daliban damar yi wa kasa hidima na NYSC ta kuma aike wa gwamnatin jihar Kano shaidar takardunsu na kammala karatu, dan haka a biya ta ragowar kudadenta da suka makale.

Kazalika jami’ar ta Crescent ta aike wa gwamnatin jihar Zamfara irin wannan wasika inda ta bukaci gwamnatin jihar ta biya bashin kudin karatun dalibanta Naira miliyan 270.