✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Ribas ta haramta wa dalibai sanya sarkar kafa

Dokar ta kuma haramta shigowa harabar makarantar a sanye da wando a sabule ba, ko suma mai rini da sauran dabi'u mara fasali.

Jami’ar Jihar Ribas da ke Fatakwal ta haramta wa dalibai mata sanya sarkar kafa da kuma yin shigar da ba ta kamata ba ga dukkanin daliban jami’ar.

Hukumar jami’ar ta ce daga yanzu haramun ne ga daliban jami’ar sanya matsattun kaya da dangalallen sikel da sanya zoben hanci da yin zane a jiki da saka dankunne ga dalibai maza da sauransu.

Sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun Rajistaranta, Dokta S.C Enyindah, ta ce dokar ta fara aiki nan take, “Kuma duk wanda aka kama ya take wannan doka, ya kuka da kansa.”

Dokar ta kuma haramta shigowa harabar makarantar a sanye da wando a sabule ba, ko suma mai rini da sauran dabi’u mara fasali.

Rajistaran ya ce, majalisar kolin jami’ar ta cimma matsayar daukar wannan mataki ne a taron da ta yi a Satumba da nufin tsaftace dabi’un dalaibai da kuma yanayin shigarsu.