✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’in DSS ya harbi matashi a taron APC a Gombe

An harbe shi ne yayin kamfen din Gwamnan Jihar

Wani jami’in tsaro na DSS ya harbi wani matashi yayin taron yakin neman zaben jam’iyyar APC a garin Bojude na Karamar Hukumar Kwami ta jihar Gombe.

Bayanai sun nuna an harbi matashin ne mai suna Auwal Hassan, mai kimanin shekara 30, yayin gangamin a ranar Lahadi.

Marigayin dai ya bi sahun sauran daruruwan mazauna garin ne da nufin tarbar Gwamnan Jihar, Inuwa Yahaya.

Shaidun gani da ido sun shaida wa Aminiya cewa marigayin ya hadu da ajalinsa ne yayin wata turereniya yayin da Gwamnan ya isa wajen taron.

Shaidun sun ce nan take matashin ya fadi yana matagugu a kasa saboda harbin, lamarin da ya tunzura sauran matasan suka fara ihun ‘ba ma yi’.

Rahotanni sun ce da kyar sauran jami’an tsaron da ke ayarin Gwamnan suka iya shawo kan matasan ta hanyar kwantar da hankulansu.

Sai dai da yake jawabi jim kadan da faruwar lamarin, Gwamna Inuwa ya ba da umarnin tsare jami’in na DSS da ya yi harbin.

Daga nan ne ya ba da umarnin a dauki matashin a kai shi asibiti kuma gwamnati za ta dauki nauyinsa.

Kazalika, Gwamnan ya sanar da nada wanda aka harba din da karin wasu mutum hudu daga garin a matsayin hadimansa.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya bukaci a ba shi lokaci don ya binciki labarin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi waiwayi wakilin namu ba.