✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya mutu bayan ya taka nakiya a Mali

An kashe shi ne yana tsaka da sintiri a kasar

Wani jami’in kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Arewacin kasar Mali mai fama da rikici, ya mutu bayan ya taka nakiya a lokacin da yake tsaka da sintiri a yankin.

Shugaban rundunar majalisar a kasar ta Mali wacce ake kira da MINUSMA, El-Ghassim Wane, ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

Jami’in dai na cikin ’yan kasar Gini da ke cikin tawagar, kamar yadda daya daga cikin dakarun da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP).

“Da farko ya ji rauni, kafin daga bisani kuma ya rasu a asibitin birnin Kidal,” inji majiyar.

Kisan jami’in dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar, a daidai lokacin da rundunar ke ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Akalla dai jami’an kiyaye zaman lafiya 175 ne suka rasa rayukansu a makamantan wadannan hare-haren.

“Wani mummunan labari na kisan abokin aikinmu ya kara yawan wadanda aka kashe a bakin aikinsu a kasar Mali,” kamar yadda El-Ghassim Wane ya wallafa a Twitter.

Nakiyoyi da bama-bamai dai na cikin abubuwan da masu ikirarin jihadi a kasar ke amfani da su wajen kisan dakarun Majalisar Dinkin Duniyar da ma na kasar ta Mali.

Bugu da kari, suna kuma kashe fararen hula da dama.

Mali dai, wacce matalauciyar kasa ce da ke yankin Sahel kuma ba ta da iyaka da teku ta yi ta fama da juyin mulki tun a ranar 20 ga watan Agustan 2021.

Rikicin kasar dai ya yi sanadiyyar mutuwar dubban fararen hula da sojoji, yayin da dubban daruruwan wasu kuma suka rasa muhallansu.

(AFP)