✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’in tsaro da wasu karin mutum 2 sun kone kurmus a hatsarin babura a Legas

Wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC da wasu mutane biyu sun kone kurmus a sakamakon wasu babura da suka yi taho-mu-gama da juna a jihar…

Wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC da wasu mutane biyu sun kone kurmus a sakamakon wasu babura da suka yi taho-mu-gama da juna a jihar Legas ranar Talata.

Hatsarin ya auku ne a kan babbar hanyar Badagry zuwa Seme.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a kan idanunsa, hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar a yankin Iyaafin wanda ya janyo tashin wutar da ta kone mutanen.

Ya ce, “Mutum biyu ne da suke a kan babura, dauke da wasu jarkoki makare da man fetur suka yi taho-mu-gama da wani jami’in hukumar NSCDC a kan babur.

“Hakan ya jawo tashin wuta nan take inda dukkansu suka kone kurmus.

“Daga bisani an kai musu dauki ta hanyar garzayawa da su babban asibitin Badagry, daga baya kuma aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas domin ci gaba da samin kulawa,” inji shi.