✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamilu Gwamna ya sake komawa PDP

Sardauna Dan uwa ne a gare ni kuma ina masa maraba da dawowa.

Sardaunan Gombe, Alhaji Jamilu Isiyaku Gwamna ya sake komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP bayan ficewar sa daga jam’iyyar APC makonni hudu da suka gabata.

Cikin wata sanwar da mai magana da yawunsa, Ibrahim Sani Shawai ya aike wa manema labarai, Jamilu Gwamna ya sanar da komawarsa jamiyyar PDP ranar Laraba a Abuja, babban birnin kasar.

Sanarwar ta nuna cewa Jamilu Gwamna ya fice daga jam’iyyar APC makonni hudu da suka gabata bai shiga kowacce jam’iyya ba sai a yanzu ya bayyana shigar sa jam’iyyar da ya bari tun farko ta PDP

Shawai, ya ce Jamilu ya bayyana shigarsa jam’iyyar PDP ne a lokacin da ya ziyarci jagoran jam’iyyar na Jihar Gombe kuma tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo a gidansa da ke Abuja.

“Mai girma Talban Gombe a yau mun ziyarce ka ne tare da magoya baya bisa dalilai guda biyu – na farko don karfafa dangartakar mu a matsayin ‘yan uwan juna sannan na sanar da kai na dawo jam’iyyar PDP” inji Jamilu gwamna

Ya ce yana mai tabbatar masa cewa za su dinke duk wata baraka su kuma hada kai don sake dawo da jam’iyyar PDP mulki a Jihar Gombe a zaben 2023 da ka tafe.

A nasa jawabin, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi godiya ga Jamilu Gwamna da tawagarsa bisa wannan ziyara, sannan ya yi masa maraba da dawowa jam’iyyar PDP, sannan ya kuma tabbatar da bashi goyon bayansa game da samun hadin kan jam’iyyar.

“Sardauna Dan uwa ne a gare ni kuma ina masa maraba da dawowa tsohon gidansa kuma ina mai sanar da kai za mu hadu don ciyar da jam’iyyar gaba da samun nasarar cin zabe.”

Kazalika, Dankwambo ya shawarci Sardaunan Gomben da ’yan tawagar magoya bayan nasa da su dawo su nemi goyon bayan jama’a tun daga tushe don ganin jam’iyyar ta lashe zaben da ke tafe na shekarar 2023.

Aminiya ta ruwaito cewa, Jamilu Gwamna ya fice daga jam’iyyar PDP bayan hana shi takarar gwamna, la’akari da ganin cewa da shi aka yi fadi tashin a jam’iyyar da har ta kai ga Inuwa Yahaya ya samu nasarar lashe zabe a 2019.