✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jamus ta fada matsin tattalin arziki’

Wani kwararre a Cibiyar Binciken Tattalin Arziki ta Jamus (DIW), Guido Baldi, ya ce cibiyar na ganin cewar kasar ta fada halin matsin tattalin arziki.…

Wani kwararre a Cibiyar Binciken Tattalin Arziki ta Jamus (DIW), Guido Baldi, ya ce cibiyar na ganin cewar kasar ta fada halin matsin tattalin arziki.

Baldi ya fada a ranar Laraba cewar akwai yiwuwar yakin da ake gwabzawa tsakanin Ukraine da Rasha ya yi sanadiyyar koma-bayan tattalin arzikin kasar da kashi biyar a shekarun 2022 da 2023.

Ya kara da cewa, tashin farashin makamashin da ake fama da shi zai haifar da asara a fannin lantarki wanda hakan babbar barazana ce ga kamfanoni da dama a kasar.

Masanin ya kuma ce hauhawar farashin makamashi da kuma rashin tabbas na ci gaba da yi wa harkokin kasuwanci tarnaki a kasar.

“Nan ba da jimawa ba tambayar da za ta kunno kai ita ce, ko kamfanoni a kasar za su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu da wannan yanayi da ake fuskanta,” inji Laura Pagenhardt wanda shi ma kwararre ne a cibiyar ta DIW.