Jamus za ta dawo wa Najeriya kayan tarihin da ta sace shekara 120 da suka wuce | Aminiya

Jamus za ta dawo wa Najeriya kayan tarihin da ta sace shekara 120 da suka wuce

Wasu daga cikin kayan tarihin da Jamus ta sace daga Najeriya
Wasu daga cikin kayan tarihin da Jamus ta sace daga Najeriya
    Sani Ibrahim Paki

Kasashen Jamus da Najeriya sun sanya hannu a kan yarjejeniyar da za ta share fagen dawo wa da Najeriyar kayan tarihin da aka sace mata zamanin mulkin mallaka, sama da shekara 120 sa suka gabata.

Da wannan yarjejeniyar dawo da kayan tarihin wadanda aka fi sani da Benin Bronzes dai, Najeriya na sa ran sauran kasashen Turai za su bi sahun Jamus din a nan gaba kadan.

A shekarar 1897 dai turawan mulkin mallaka na Ingila suka wawushe kayan tarihi da dama, mallakin masarautar Benin da ke Jihar Edo ta yanzu.

Daga bisani an warwatsa kayayyakin zuwa kasashen Turai daban-daban.

Kazalika, an sayar da wasu daruruwan kayan kuma ga gidajen tarihi kamar na birnin Berlin a Jamus, wanda a can ne akasarin kayan masarautar ta Benin suke.

An dai kiyasta cewa akwai irin wadannan kayayyakin tarihin a gidan tarihin na Berlin kimanin 530, ciki har da wasu guda 440 na azurfa.

Akasarin wadannan kayayyakin an kera su ne tun tsakanin karni na 16 zuwa na 18.

Ministar Harkokin Wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce, “Wannan somin-tabi ne na dawo da kayan tarihin sama da 1,000 da ke gidajen tarihin kasar Jamus, wadanda dukkansu mallakin mutanen Najeriya ne.

“Ba daidai ba ne mu dauki wadannan kayayyakin na azurfa, ba daidai ba ne mu ajiye su tsawon shekara 120.

“Wadannan kayan tarihin na daya daga cikin wasu manyan abubuwan alfaharin Afirka, amma kuma suna bayar da labarin tarihin mulkin mallaka,” inji ta.

Gwamnatoci da gidajen tarihi da dama a kasashen Turai da Arewacin Amurka sun yi ta neman kawo karshen takaddamar kayan tarihin da aka sace zamnin mulkin mallakar.

A bara ne dai Jamus ta bayyana aniyarta ta dawo wa da Najeriya kayan tarihin da ke cikin kasarta.

Ko da yake dai kasar ba ta bayyana zuwa yaushe ne za ta dawo da kayan ba, amma ta ce hakan zai zo ne a cikin shekarar nan.