✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jamus za ta halasta wa wadanda suka mallaki hankali shan tabar wiwi

Jama'a na iya saya ko mallakar Gram 20 har zuwa 30 na tabar wiwi.

Gwamnatin Jamus ta amince da tsarin halarta tabar wiwi ga wadanda suka zarta shekaru 18 da haihuwa.

Sai dai gwamnatin ta ce tana jiran sahalewar fannin shari’a na kotun Turai a kan wannan batu domin aiwatar da shi a shekara ta 2024.

A wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Berlin, Ministan Kiwon Lafiya na Jamus, Karl Lauterbach ya ce wannan yana nufin cewa jama’a na iya samarwa da yin kasuwancin tabar wiwi, tare da saya ko mallakar Gram 20 har zuwa 30 na wannan taba.

A shekara ta 2024 ne dokar halarta tabar wiwi za ta fara aiki a Jamus idan komai ya tafi salin-alin.

Wannan sassaucin zai sanya Jamus zama daya daga cikin kasashen Turai da suka soke haramcin shan taba wiwi.

Burin da fadar mulki ta Berlin ta sa a gaba, shi ne tabbatar da kariya a fannin kiwon lafiya da kuma dakile laifuka da ke da nasaba da kasuwar taba wiwi ta bayan fage.