✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jamus za ta sanya wa masu amfani da iskar gas sabon haraji

Farashin makamashi ya fara tashin gwauron zabo a Jamus, bayan gwamnatin kasar ta ba da sanarwar yiwuwar sanya harajin Dala 2.4  kan dukkanin kilo na…

Farashin makamashi ya fara tashin gwauron zabo a Jamus, bayan gwamnatin kasar ta ba da sanarwar yiwuwar sanya harajin Dala 2.4  kan dukkanin kilo na iskar gas.

Farashin makamashin ya zamo babban batun siyasa a bangaren tattalin arzikin nahiyar Turai, baya ga tsadar rayuwa da ta yi tashin gwauron zabo sakamakon yakin Ukraine da Rasha.

Haka zalika, yakin kasashen biyu ya sanya Rashan ta rage yawan iskar gas din da ta ke fitarwa, yayin da yanayin sanyi ya kankama a yankin.

Bayanin adadin kudin harajin ya bulla ne daga kungiyar masu rarraba iskar gas daban-daban da ke kasar.

Haka kuma, gwamnatin ta ce ta sanya harajin ne da nufin taimaka wa ‘yan kasar da ke shigo da iskar gas din, bayan sun siyo shi da tsadar gaske daga wasu kasashen da ba Rasha ba, da hakan ke haifar musu da asara mai yawa.

Harajin dai zai fara aiki ne a dokance daga ranar daya ga watan Oktoban 2022, sai dai a hukumance ba za a fara aiki  da shi ba har sai watan Nuwamba ko Disamba domin cika ka’idojin kare masu amfani da canjin farashin.

Jimillar harajin makamashin zai iya kai wa kusan Yuro 484, kuma hakan zai sa a samu hauhawar farashin kayayyaki bayan iskar gas din.