✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janye gayyata: El-Rufai ya caccaki kungiyar lauyoyi

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kakkausan suka ga Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), bayan ta soke gayyatar da ta yi masa ya yi jawabi a…

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kakkausan suka ga Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), bayan ta soke gayyatar da ta yi masa ya yi jawabi a babban taronta da ke tafe.

NBA ta soke gayyatar ne bayan wasu ‘ya’yanta sun yi barazanar kaurace wa taron bisa hujjar cewa bai dace gwamnan ya yi jawabi ba, saboda matsalar kashe-kashe a jiharsa.

Biyo bayan takardar koken da wani lauya mai suna Usani Odum ya gabatar ne kungiyar ta janye gayyatar ka kuma sanar da gwamnan.

A martaninsa, El-Rufai ya ce hakan bai dame shi ba; hasali ma ba shi ya nemi ya yi jawabi a taron ba, don haka ko a jikinsa.

Ya kuma yi barazanar daukar matakin da ya dace a kan abin da ya kira cin mutunci da ke cikin takardar koken da aka rubuta a kansa.

“Ko da yake NBA ce ta bukaci ya yi jawabi a taron, Malam Nasir El-Rufai na so a fahimci cewa bai damu ba don ya rasa damar yin jawabin”, inji kakakinsa Muyiwa Adeleke.

Ya ce da ma abokan gwamnan lauyoyi ne suka nemi ya yi bayani a zaman tattaunawan taron kan zama dan kasa, shi kuma ya amsa.

Amma “ko ba a mimbarin NBA ba, ya kamata a ci gaba da tattauna batun, kuma zai ci gaba da yin magana a kan abubuwan da kasa ke bukata domin samun cigaba”.

Sai dai ya soki kungiyar wadda ke aikin tabbatar da adalci, kan yadda ta karkata ga matsayin masu korafin ba tare da saurarar bangaren shi wanda ake zargin ba.

Ya ce gwamnan ya dauki matakai da dama ta fuskar tsaro da hukumomi da kuma fasahar zamani domin kawo karshen rikice-rikice a jihar.

“Ya yi hakan cikin adalci ga mazauna, ba wai ga masu shiga kafafen yada labarai ba, da ke bin son ransu ko da kuwa su ne musabbabin matsalolin.

“Masu neman cewa Jihar Kaduna ce kadai ke fama a matsalar tsaro a Arewa maso Yamma, ko kuma wani bangare na jihar ne kadai ke da matsalar suna yaudarar kansu.

“El-Rufai ya yi tsayin daka domin ganin ya kawo karshen zubar da jini da asarar dukiyoyi na babu gaira babu dalili”, inji shi.