✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jaruma Fati Muhammad tana samun sauki

Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood Fati Muhammad wadda ta yi jinya a wani asibiti da ke garin Kaduna ta samu sauki. A ranar Alhamis ce aka…

Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood Fati Muhammad wadda ta yi jinya a wani asibiti da ke garin Kaduna ta samu sauki.

A ranar Alhamis ce aka fara rade-radin cewa jikin tsohuwar jarumar ya yi zafi.

Aminiya ta ci karo da rubutun da Fatim Muhammad ta wallafa a shafinta na Instagram, inda take cewa, “Alhamdulillahi. Ina samun sauki sosai. Allah na gode maKa. Ina godiya matuka da addu’o’inku,” inji ta, inda ta ambaci sunan Ali Nuhu da Hadiza Gabon da Ali Jita da mawaki Aimskid