Jarumar Kannywood, Maryam Waziri, ta amarce da Tijjani Babangida | Aminiya

Jarumar Kannywood, Maryam Waziri, ta amarce da Tijjani Babangida

Jaruma Maryam Waziri
Jaruma Maryam Waziri
    Isiyaku Muhammed

Jarumar Kannywood, Maryam Waziri ta cikin shirin Labarina ta amarce a ranar Juma’a.

Maryam, dai ita ce ta fito da sunan Laila a shirin Labarina mai dogon zango.

Daraktan shirin Labarina, Malam Aminu Saira ne ya wallafa hakan a shafinsa na Instagram, inda ya ce, “A madadina da kamfanin Saira Movies, muna taya ’yar uwa Maryam Waziri murnar auren da ta yi yau [Juma’a].

“Allah Ya ba su zaman lafiya. Allah kuma Ya ba su zuriya dayyiba. Muna taya murna. Muna rashinki dinki Laila.”

A kasan rubutun na Aminu Saira, Maryam Waziri ta mayar da martani, inda ta ce, “Amin Ya Hayyu Ya Qayyum. Na gode sosai. Ba zan manta da Saira Movies ba.”

Tijjani Babangida dai tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Super Eagles ne.