✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin fim din ‘Black Panther’ Chadwick Boseman ya rasu

Jarumin fim dan kasar Amurka Chadwick Boseman, wanda ya yi fice a fim din Black Panther, ya rasu. Sanarwar rasuwar Chadwick, ta jefa masoya da…

Jarumin fim dan kasar Amurka Chadwick Boseman, wanda ya yi fice a fim din Black Panther, ya rasu.

Sanarwar rasuwar Chadwick, ta jefa masoya da masu harka a masana’atar fim a fadin duniya cikin alhini.

Mai shekara 43 din ya rasu ne a Los Angeles sakamakon cutar kansa da ya shekara hudu yana fama da ita.

Amma bai taba tattauan batun rashin rafiyar tasa a bainar jama’a ba, yayin da ya ci gaba yi aikin manyan finafinan Hollywood a yayin da sau dama aka masa tiyata, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Sakon rasuwar da suka fitar ya ce “Chadwick, Mayakin gaske ya jure cutar har ya kawo muku fina-finai da dama da ke matukar kauna”.

Iyalan sun ce fina-finansa na Marshall, Da 5 Bloods, August Wilson’s Ma Rainey’s Black Bottom da sauransu duk an yi su ne a tsakanin lokutan da aka yi masa tiyata.

“Babbar karamcin da ya samu a tarihin rayuwarsa na jarumi shi ne matsayin da ya samu na farkar da Sarki T’Challa a fim din Black Panter, inji sanarwar.

Shaharar Boseman

A 2013 Boseman ya fara yin fice ne a 2013 bayan ya fito a fim tare da fitaccen dan wasan kwallon baseball, Jackie Robinson a fim din 42.

Sai kuma a 2014 da ya fito a fim din Get on Up tare da mawaki James Brown.

Amma za a fi tuna shi da fim din Black Panther, daya ga cikin manyan finafinan 2018.

A cikin fim din Boseman ya fito a matsayin sarkin Wakanda, wani garin ‘yan Afirka wanda ya fi ko’ina ci gaban fasa a duniya.