Jarumin fina-finan Amurka, Arnold Schwarzenegger ya yi hatsarin mota | Aminiya

Jarumin fina-finan Amurka, Arnold Schwarzenegger ya yi hatsarin mota

Arnold Schwarzenegger
Arnold Schwarzenegger
    Sani Ibrahim Paki

Jarumin nan na masana’antar fina-finai ta Hollywood, kuma tsohon Gwamnan Jihar California da ke Amurka, Arnold Schwarzenegger ya yi hatsarin mota.

Kakakin jarumin ya tabbatar wa jaridar Los Angeles Times cewa hatsarin ya faru ne ranar Juma’a a birnin Los Angeles, kuma ’yan sanda sun tabbatar da jikkatar mutum daya.

Kazalika, jaridar ta wallafa hotunan wajen da hatsarin ya faru, inda aka ga motarsa kirar SUV a kan wasu motocin guda biyu, shi kuma yana tsaye a gefe.

Kakakin ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da Schwarzenegger yake tuka motar tasa kirar SUV.

Motar dai tasa ta yi kuli-kulin Kubura ne a tsakiyar hanya sannan ta doki ragowar motocin biyu.

Tuni dai aka garzaya da wani mutum daya zuwa asibiti, bayan ya samu kananan raunuka.

Schwarzenegger dai bai ji rauni ba, amma kakakin nasa ya ce yana bibiyar halin da wanda ya ji raunin yake ciki a asibiti.