✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin Nollywood Papa Ajasco ya rasu

Mista Ogunrombi ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim din Papa Ajasco.

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina–finai ta Kudancin Najeriya ta Nollywood, Femi Ogunrombi wanda aka fi sani da Papa Ajasco, ya rasu.

Wani mai ruwa da tsaki a harkokin wasan kwaikwayo, Husseini Shaibu ne ya tabbatar da rasuwarsa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

Ya rubuta cewa, “A yanzu na samu labarin cewa masanin kida, tsohon mai koyar da waka  a NATIONALTROUPE kuma wanda ya fito a matsayin ‘Papa Ajasco’ a cikin shahararren shirin barkwanci na #waleadenugaprod ‘Papa Ajasco’, Mista Femi Ogunrombi ya rasu.

“An sanar da ni cewa dan wasan kwaikwayon, mawaki, babban jarumi kuma kwararren ma’aikacin jinya wanda muke kira ‘Uncle Ogurombo’ ya rasu a Yammacin yau (Asabar).”

Mista Ogunrombi ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim din nan na barkwanci mai dogon zango wanda Wale Adenuga ya shirya mai suna Papa Ajasco.

Ogunrombi ya fito a matsayin Papa Ajasco a cikin shirin mai wannan suna bayan ya maye gurbin Abiodun Ayoyinka da aka soma fim din da shi.