✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jawabin Buhari na sabuwar shekara ba shi da alkibla – PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na sabuwar shekarar 2021 a matsayin fanko

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na sabuwar shekarar 2021 a matsayin fanko kuma mara alkibla.

Ta kuma ce jawabin ya kara nunawa a fili cewa kasar ba ta da shugabanci.

PDP a wata sanarwa da Sakataren Watsa Labaranta, Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Juma’a ta ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su tashi tsaye domin ceto kasar daga tafarkin durkushewa.

A cewarta, kamata ya yi jawabin nasa ya fi mayar da hankali kan batun kalubalen tsaro dake addabar kasar a halin yanzu, musamman ta fuskar sauya fasalinsa, kamar yadda ‘yan kasa ke ta yin kira.

Sai dai jam’iyyar ta ce abin takaici ne yadda shugaban ya bige da zarge-zarge marasa tushe ballantana makama da kuma alkawuran da ba za su magance komai ba.

PDP ta kuma ce, “Tarin korafe-korafen da suke cikin jawabin na nuna raunin shugabanci da gazawa wurin magance kalubalen ’yan bindiga, ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da kuma rikice-rikicen addini da na kabilanci.

“Ta fuskar tattalin arziki ma, shugaban ya gaza fito da wani sahihin tsari da zai ceto kasar daga mawuyacin halin da ta fada.

“Ba shi da wata alkibla ta dawo da darajar Naira, biyan tarin basukan da ake bin mu, farfado da asusun ajiyar mu na kasashen ketare, bayar da kwarin gwiwa ga masu zuba jari na waje, samar da ayyuka, samar da wadataccen abinci da kuma tsarin kiwon lafiya.

“Halin da kasarmu ke ciki a yanzu na bukatar jajirtaccen shugaba ba wai wanda zai harde kafa a kan kujera yana jiran gyara ya zo daga sama ba.

“Jam’iyyarmu na Allah-wadai da yadda a cikin jawabin shugaban ya gaza fayyace makomar matasan da aka ci zalinsu saboda sun yi zanga-zangar EndSARS, ko kuma ya kafa kwamitin shugaban kasa domin bincikar zargin kashe mutane a Lekki,” inji PDP.