✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP da APC Danjuma ne da Danjummai —Jega

Jega ya ce dole a samar da jam'iyyar mutane masu gaskiya.

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya gargadi ’yan Najeriya da kada su sake amincewa da jam’iyyun APC da PDP, inda ya ce sun gaza kawo canji cikin shekara 20 da suka yi a kan mulki.

Jega yana magana ne game da babban zaben 2023 da ke tafe, inda ya shawarci ’yan Najeriya da su sauya akala muddin suna son samar wa da kasar ci gaba.

A wata hira da sashen Hausa na BBC a ranar Litinin, Jega ya ce mummunar rawar da jam’iyyun biyu suka taka a tsawon shekaru ya nuna karara cewa babu bukatar a sake amincewa da su.

Tsohon shugaban Hukumar zaben ya ce “Jam’iyyun APC da PDP duka sun mulki kasar nan amma babu wani gyara da suka samar. Idan ka duba yaki da cin hanci da rashawa, duk mutanen da aka ce barayi ne kuma za a hukunta su saboda sun yi sata a PDP, yanzu sun koma APC, kuma babu abin da ya same su.

“Shi ya sa muka yi imani lokaci ya yi da za a samar da wata inuwa ga duk mutanen kirki su shiga, kuma su ba da gudunmawa wajen kawo canji a Najeriya.

“Don haka, wannan ne dalilin da ya sa na riga na yi rijista da PRP a matsayin dan jam’iyyar don taimaka wa Najeriya,” cewar Jega.

POPCAST:

Ya kuma ce lokaci ya yi da ya kamata a matsayinsu na malamai su tashi tsaye wajen kawo sauyi a Najeriya.

Farfesa Jega ya ce, “Ko da kai mutumin kirki ne, kuma kana cikin jam’iyyarsu, ba za ka iya yin komai ba, to ya kamata a samu wata jam’iyyar ta daban wacce za ta hada mutanen kirki tare da yin aiki don ceto kasar nan,” inji shi.

“Na fara koyarwa a matsayin malamin jami’a tun 1979, yanzu shekara 40 ke nan, don haka abin da na karanta kuma na lura da shi a lokacin da nake shugabantar hukumar INEC, da kuma yadda ’yan siyasarmu ke sauyawa bayan lashe zabe abin tsoro ne. Yadda suke tafiyar da mulkin kasar nan shi ma gaskiya abin tsoro ne.”

Tsohon shugaban na INEC ya kuma danganta matsalolin da ke addabar Najeriya da rashin shugabanci, lamarin da a cewarsa, shi ne ya sa wasu ke kira da a raba kasar.