Taliban ta sanar da jami’an sabuwar gwamnatinta a Afganistan, wadda Mullah Hasan Akhund, na hannun daman marigayi Mullah Omar, wanda ya kafa kungiyar, zai jagoranta a matsayin mukaddashin Firayim Minista.
Mai magana da yawun kungiyar, Zabihullah Mujahid, ya ce duk mutanen da aka bayyana sunayen nasu za su rike mukaman ne a matsayin masu rikon kwarya.
Ga cikakken jerin da jami’an gwamnatin da kungiyar ta wallafa a ranar Talata
- Firai Minista – Mullah Mohammed Hasan Akhund
- Mataimakin Firai Minista na 1 – Mullah Abdul Ghani Baradar
- Mataimakin Firai Minista na biyu – Mawlavi Abdul Salam Hanafi
- Ministan Harkokin Waje – Mawlavi Amir Khan Muttaqi
- Ministan Tsaro – Mawlavi Mohammed Yaqoob
- Ministan Cikin Gida – Mullah Sirajuddin Haqqani
- Ministan Shari’a – Mawlavi Abdul Hakim Sharie
- Ministan iyaka da Kabilanci – Mullah Noorullah Noor
- Shugaban Leken Asiri – Mullah Abdul Haq Wasiq
- Ministan Kudi – Mullah Hedayatullah Badri
- Ministan Tattalin Arziki – Qari Din Mohammed Hanif
- Gwamnan Babban Bankin – Haji Mohammed Idris
- Ministan Makamashi da Ruwa – Mullah Abdul Latif Mansoor
- Ministan Raya Karkara – Mullah Younus Akhundzada
- Ministan Ayyukan Jama’a – Mullah Abdul Manan Omari
- Ministan Ma’adanai da Man Fetur – Mullah Mohammed Esa Akhund
- Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu – Mullah Khairullah Khairkhwah
- Mataimakin Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu – Zabihullah Mujahid
- Ministan Sadarwa – Mawlavi Najibullah Haqqani
- Ministan Ilimi Mai Zurfi – Abdul Baqi Haqqani
- Ministan ’Yan Gudun Hijira – Haji Khalil ur Rahman Haqqani.