✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin ’yan takarar Shugaban Kasa 18 da za su fafata a Zaben 2023

Za a gudanar da zaben Shugaban Kasa a ranar 25 ga Fabrairun badi.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar Shugaban Kasa 18 da na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a dukkan jam’iyyun kasar nan da za su fafata a zabubbukan 2023.

Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talatar da ta gabata, inda ta ce jerin na kunshe ne da sunayen ’yan takara daga jam’iyyu 18.

An wallafa jerin sunayen ’yan takarar daga dukkan mazabun kasar nan a shafin Intanet na Hukumar INEC.

Jadawalin babban zaben kasar nan dai ya nuna za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisun Dokoki na Tarayya ne a ranar 25 ga Fabrairun badi, sai na gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi a ranar 11 ga Maris.

’Yan takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu 18 sun fito ne daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ’yan takarar majalisun dokoki na kasa daga jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja.

Baya ga sunayen ’yan takarar da Hukumar INEC ta wallafa, ta kuma bayyana jinsi da shekaru da matakin ilimi na kowane dan takarar.

Mutum 4,223 ne suke takarar neman kujera a Majalisar Dokoki ta Kasa da ta hada da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai masu kujeru 469.

Kwamishinan Hukumar INEC ta Kasa kan Labarai da Ilimantar da Masu Zabe, Barista Festus Okoye wanda ya bayyana haka ya ce, mutum 1, 101 ne suke takarar kujerun sanatoci 109, yayin da mutum 3,122 suke takarar kujerun Majalisar Wakilai 360.

Sai dai ba a san makomar takarar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, wand sunansa bai fito a jerin sunayen ’yan takarar ba, kamar yadda sunan mai kalubalantarsa Machina bai fito ba a Mazabar Yobe ta Tsakiya.

Amma sunayen Sanata Godswill Akpabio daga Akwa Ibom da Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi sun bayyana a jerin duk da suna fuskantar matsala iri daya ce da Sanata Ahmed Lawan.

Yanzu haka ana kotu a tsakanin bangaren Sanata Lawan da Bashir Machina kan wanda zai tsaya wa APC takarar Sanata a Yobe ta Arewa.

Haka bangaren Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya sha kasa inda bau ko daya daga cikin masu takara a karkashin bangaren da ya haye don tsayawa takarar kowace kujera a Majalisar Dokoki ta Kasa.

Wannan yana zuwa ne bayan da Hukumar INEC ta karbi ’yan takarar bangaren Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Shiyyar Kudu maso Kudu, Mista Dan Orbih, wanda kotu ta tabbatar da cewa shi ne sahihin bangaren PDP da doka ta amince da shugabancinsa.

Sai dai komai yana iya canjawa idan Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin da ya saba wa kotun baya.

Jerin karshe na ’yan takarar Shugaban Kasa a zaben na 2023 yana dauke da sunayen masu neman zama Shugaban Kasar da suka hada da Imumolen Christopher, Accord Party (AP) da Al-Mustapha Hamza, Action Alliance (AA) da Sowore Omoyele, African Action Congress (AAC) da Kachikwu Dumebe, African Democratic Congress (ADC) da Sani Yabagi Yusuf, Action Democratic Party (ADP) da Tinubu Bola Ahmed, All Progressibes Congress (APC).

Sauran su ne, Umeadi Peter Nnanna, All Progressives Grand Alliance (APGA) da Ojei Princess Chichi, Allied People’s Movement (APM) da Nnamdi Charles Osita, Action Peoples Party (APP) da Adenuga Sunday Oluwafemi – Boot Party (BP) da Obi Peter Gregory, Labour Party (LP) da Musa Rabi’u Kwankwaso, New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Osakwe Felix Johnson, National Rescue Movement (NRM) da Abubakar Atiku, Peoples Democratic Party (PDP).

Sai Abiola Latifu Kolawole, Peoples Redemption Party (PRP) da Adebayo Adewole Ebenezer, Social Democratic Party (SDP) da Ado-Ibrahim Abdumalik, Young Progressibes Party (YPP) da kuma Nwanyanwu Daniel Daberechukwu, Zenith Labour Party (ZLP) Hukumar INEC ta ce a cikin ’yan takarar mukaman daban-daban akwai nakasassu 11.