Daily Trust Aminiya - JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (11)
Subscribe

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (11)

An kawata zauren da kwalliya, ga fitilu nan na haskawa iri-iri. Idan ja ta kunna ta mutu sai bula ta kunna, ita ma idan ta mutu sai dorawa ta kunna. A kan dandamali kuwa, teburin DJ ne a girke, dauke da kwarankwacaman kayan kida na zamani iri-iri. Sautin kida da waka ya mamaye sarari da kewayen harabar zauren taron. Babu mai jin wani batu ko sauti, idan ba rugunniyar kida da wakar da ke fitowa daga manya-manyan lasifikokin da aka girke a zauren ba.

A daidai lokacin ne Binta da kawarta Saratu suka shigo zauren. Alhaji Baba ne ya kawo su a motarsa, inda shi ma ya samu wuri ya zauna.

Su kuwa suka shiga cikin rukunin kawayensu, suka ci gaba da gaisawa. Bayan Binta ta shigo zauren, kasancewar ita ake jira, a matsayinta na uwar biki, sai DJ ya kashe kayan kidansa. Zauren ya yi shiru, kamar mutuwa ta gitta.

“Wacce ake jira ta zo, ba tare da bata lokaci ba, za mu ci gaba da gudanar da ajandar wannan gagarumin biki.” Muryar mai gabatar da taro ce ta fara amo a cikin zauren.

“Kamar yadda mahalarta suka sani, yau ce ranar haihuwar Binta Balarabe, rana ce ta farin ciki da murna.”

Mai gabatarwa ya ci gaba da bayani, yana yi yana duba wata gajeruwar takarda da ke rike a hannunsa, yana karanto sunayen manyan baki, yana gayyatarsu zuwa wuri na musamman da aka ware musu.

Bayan an natsa, DJ ya sanya kida, kawayen Binta maza da mata suka hau dandamali suna cashewa da rawa. An samu kimanin minti biyar a haka, kafin daga bisani aka dakatar da kida.

Mai gabatarwa ya amshi kurtun magana ya fara bayani.

“A daidai wannan lokaci, a daidai wannan gaba, ina gayyatar babbar kawar uwar biki, Saratu da saurayinta, Alhaji Baba su fito fili, domin taya aminiyarsu murnar zagayowar wannan muhimmiyar rana.”

A lokacin da ya tsaya da magana, DJ ya sako wata wakar taushi, sannan mai gabatarwa ya ci gaba da magana. “A tare da wannan biki, DJ zai gabatar da sabuwar waka, wacce Bashir Yahuza Malumfashi ya rubuta mai taken “Fure.” Wannan waka, an sadaukar da ita musamman ga aminan Binta, wato ga su nan a dandamali a tsaye, Alhaji Baba da amaryarsa nan gaba kadan insha Allah, Hajiya Saratu.”

Yana rufe baki sai DJ ya sako kida, inda sabuwar wakar ‘Fure’ ta fara tashi, ta mamaye zauren gaba daya. Su kuwa Saratu da Baba suka ci gaba da takawa:

***

Fure, yeee fure!

Fure, wooo fure!

*

Ya ke masoyiyata,

Zo ki amshi fure.

*

Iska ta taso,

Ta watsa fure.

*

Maza dauko kwando,

Zo mu tsinki fure.

*

Zo miko hannu,

Sai ki damki fure.

*

Ya ke ruhina,

Ko kin san fure?

*

Zuciya mai tsafta,

Kin san ta fi fure.

*

Ya ke abin kauna,

Ke ce ruhin fure.

*

Zuciyata na ba ki,

Kin san ta fi fure.

*

Alkawari na dauka,

Za mu raya fure.

*

Duk wuya runtsi,

Za mu shaki fure.

*

Zo nan ga kore,

Hada shi da jan fure.

*

Duniya tai dadi,

Kanshi sai fure.

*

Rayuka sun haska,

Danshin kasar fure.

*

Jure fari sai tofa,

Ni ne naki fure.

*

Damina mai dadi,

Ita ke raya fure.

*

Mui nazari mai kyau,

Don mu samu fure.

*

Ga wata jaka can,

Wa zai ba ta fure?

*

Ga wata ballagaza,

Ta yi rashin fure.

*

Waccan kucakar fa?

Ta yi asarar fure.

*

Waccan mai homar,

Ba ta samun fure.

*

Kai kyale butulu,

Ba a ba ta fure.

*

Na ce ba a ba ta fure,

Ba a ba ta fure!

***

More Stories