JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (22) | Aminiya

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (22)

     Bashir Yahuza Malumfashi

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Yanzu ne na tuno da nasihar da wani malami ya taba yi mana. Abin da ya fada mana gaskiya ce. Ya ce budurcin ’ya mace shi ne babban arzikinta, shi ne rayuwarta, shi ne sirrinta kuma shi ne diyaucinta. Matukar ba mijinta na aure ne ya cire shi ba, to mace za ta kasance cikin takaici har karshen rayuwarta. Macen duk da ta yi asarar budurcinta a rariya, ta yi wa zuriyarta tabo, tun daga danta na farko har zuwa tattaba kunnenta na karshe. Gaskiya na cuci kaina, na cuci zuriyata, ba zan taba yafe wa Dandauda ba!” Saratu ta kara yin shiru, a lokacin da Binta ta ma rasa abin da za ta fada mata. Ga ci gaba:

 

Koda ta ga hankalin kawarta ya tashi sosai har tana neman shiga wani kunci marar iyaka, nan take Binta ta samo wasu hikimomi da ta bi ta sama wa Saratu sauki. Ta bayyana mata matakin da ya kamata su dauka dangane da wannan cikin shege da Malam Dandaula ya yi mata.

A lokacin da kawayen biyu suka fito daga gida, Binta na yi wa Saratu rakiya, a nan ne suka ci gaba da tattauna sauran al’amura.

“Kin ga har na so na mance da matsalata ta biyu, wacce ita ma babba ce.” Saratu ta jawo hankalin kawarta, a yayin da take kara gyara zaman jikkarta a kafada.

“Wace matsala ce kuma ta biyu?”

“Lokacin da na zo dazu, ai na shaida maki cewa abubuwa biyu ne suka taru suka yi wa rayuwata daurin gwarmai. Duk tsawon zamanmu, ai matsala daya muka yi ta kai-komo cikinta, wato matsalata da Malam Dandaula. To, daya matsalar ita ce ta soyayyata da Alhaji Baba.” Saratu ta dan dakata da magana, lokacin da suke tsallake titi, suna ta waige-waigen hagu da dama, domin samun tabbacin babu mota ko babur din da ke tahowa.

“Ina jin ki, shi kuma wace matsala ce ke tsakaninku?”

A nan ne Saratu ta bayyana mata yadda Alhaji Baba ya dauki lokaci bai kira ta a waya ba tun bayan rabuwarsu a ranar da suka halarci bikin zagayowar ranar haihuwarta. Ta sanar da ita yadda hankalinta ya tashi, ta yi ta fadi-tashin zuwa shagonsa na Kantin Kwari amma da kyar ta samu labarin abin da yake ciki.

Ta sanar da kawarta labarin da ta samu, yadda tashin hankali ya hada Alhaji Baba da uwargidansa Farida, wacce har ta yi yaji da kyar aka samu sasanci.

“Ko kin san duk wannan sabani da ya faru tsakaninsu, sanadiyyar soyayyata da shi ne?” Saratu ta rike baki cikin mamaki, lokacin da ta ci gaba da magana.

“Yanzu maganar da ake ciki, Alhaji Baba ya baza mutanensa cikin sirri wai domin su binciko masa bayani game da ni. Wannan na cikin sharadin sasanci da aka yi tsakaninsa da matarsa. An bayyana masa cewa ko zai ci gaba da neman aurena, dole sai ya yi bincike mai zurfi game da gidanmu, yanayin rayuwata da sauransu.”

“To fa!” Binta ta zaro idanu da alamar fargaba. “Lallai kam yanzu ne na kara fahimtar matsalar da kike ciki. To amma ke wa ya sanar da ke wannan labari?”

“Wallahi gaskiya ce, domin na samu tabbaci sosai. Kin san har sai da na ba da cin hanci kafin ma a yarda a ba ni labarin nan? Lokacin da hankalina ya tashi, ganin cewa kamar Alhaji Baba ya share ni, ai na je kantinsa na kasuwa fiye da kirga, amma ban samu ganawa da shi ba. Amintaccen yaronsa ne ya yarda cikin sirri ya bayyana mini duk abin da ake ciki. Sai da na ba shi Naira dubu biyu sannan ya ba ni labarin nan. Kuma shi ne ma ya ba ni shawarar da in yi taka-tsantsan, domin ana nan ana bincike game da rayuwata. To yanzu idan suka gano cewa na yi cikin shege, yaya batun nan zai kasance?” Tare da wani zazzafan hawaye a kumatunta ta kammala wannan bayani.

“Babu shakka akwai tashin hankali a nan amma duk da haka, ki kwantar da hankalinki; ki fawwala dukkan al’amarinki ga Allah. Ki sani cewa duk abin da zai faru da mutum, Allah Ya gama tsara shi, babu mai iya kauce wa kaddara. Idan akwai rabon ku yi aure da Alhaji Baba, wallahi duk duniya babu wanda ya isa ya hana. Kuskure ne ya riga ya faru, kin samu ciki a rariya. Yanzu mafita ake nema ba kuma abin da zai kara miki matsala ba.”

Da wadannan kalamai Binta ta samu kwantar wa Saratu hankali. Ta samu natsuwa har suka tare motar A Daidaita Sahu, ta shiga ta zauna.

“Kawalli na gode, na gode da wadannan shawarwari da kika ba ni,” inji Saratu, a lokacin da ta gyara zama a mota. “Da ba don ke ba, ban san yadda zan kasance ba. Na gode, Allah Ya saka da alheri, Allah Ya bar amanarmu.”

Da haka suka yi sallama, direba ya murza motarsa bisa hanya. Saratu ta waigo tana daga wa kawarta hannu har suka bace.

Za mu ci gaba