JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (25) | Aminiya

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (25)

    Bashir Yahuza Malumfashi

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Kai Danliti, yi maza ka kira mana Malam Bala, ka ce don Allah ya taimaka da mota, za mu kai yarinya asibiti.” Mahaifin Saratu ne yake umartar kaninta…” Ga ci gaba:

Lokacin da aka isa asibiti, kai-tsaye aka ba ta gado, bayan likita ya zo ya shiga aikin duba ta. Ko kafin likitan ya zo, an dauki lokaci mai tsawo ana jiransa, inda wata Nas ta rika kula da ita. Bayan dan lokaci, sai ya fito da wata doguwar takarda, wacce a cikinta ya rubuta sunayen abubuwan da yake bukatar a sayo masa, wadanda suka hada har da magunguna. Mahaifin Saratu ne ya amshi takardar ya tafi, a yayin da ya bar kawarta Binta tana kula da ita.

“Ina mijinta yake?” Abin da likita ya tambaya ke nan, lokacin da ya kalli Binta, wacce take zaune a kujera a bakin gadon da kawarta ke kwance.

Bai jira ta ba shi amsa ba sai ya ci gaba da magana. “Sai dai a yi hakuri, cikin da take dauke da shi ya zube, sakamakon kaduwa da firgici da ta samu a lokacin da kuka ce ta fadi kasa.”

“Da gaske, likita?” Da murmushi Binta ta fadi haka, a yayin da likita ya shiga mamaki da ya ga haka.

“Yaya na ga kina murna da wannan labari, wanda ya kamata a ce na bakin ciki ne?,” inji likita cikin mamaki.

“Ba za ka gane ba, amma don Allah ka kasance daya daga cikin wadanda za su rufa wa kawata asiri. Ba ta da miji, saurayinta ne ya yi mata wannan ciki kuma labarin abin da ya faru da shi ne ma ya saka ta cikin wannan larura.”

“To fa!,” inji likita, ya yi tsaye sototo kamar wanda aka cire wa laka.

“Wannan labarin abin farin ciki ne ga kawata da ni kaina. Amma iyayenta ma ba su san tana da cikin nan ba. Babu wanda ya sani, daga ita sai ni, sai kuma saurayin nata, wanda jiya ya rasu. Don haka, don Allah ka bar maganar cikin nan a ranka, kada ma ka bayyana shi ga iyayenta, idan sun zo an jima.

“Shi ke nan, babu komai, Allah Ya kiyaye gaba. Ai duk wanda ya rufa wa dan uwansa asiri, shi ma Allah zai rufa nasa.” Abin da likita ya fada ke nan, a lokacin da ya fita daga dakin jinya, ya nufi ofishinsa.

***

Alhaji Baba ya isa gida cikin gajiya lilis, da ma tun a shago ya yi ta korafi kuma ya rasa abin da ke masa dadi a wannan rana. Yaran shagonsa sun yi la’akari da yadda yake ta cika yana batsewa da fushi. Magana kadan za su yi masa sai ya hau su da fada. Sun rasa musabbabin wannan canjin yanayi na maigidansu.

Tun bayan da aka gama jam’in La’asar da shi, ya shaida wa yaransa cewa zai tafi gida, idan lokaci ya yi su kulle shagon. Koda ya shiga mota, babu abin da yake tunani sai lamarin rayuwa kuma duk tunanin da ya zo masa ba ya zama sai ya wuce kamar gilmawar walkiya, sai kuma wani ya bijiro. Yana tsakar tafiya ne a tukin kilomita 60 a awa sai wayarsa ta kada, alamar an bugo masa. Ya sanya hannu ya dauko ta daga gaban aljihu. Ya duba fuskar wayar sai ya ankara cewa kawar budurwarsa ce ke kiransa.

Ya buga wani uban tsaki kamar tsaka, ya sanya hannu ya danna maballin kashe wayar. Ya mayar da ita aljihu. “Aikin banza!” Abin da ya fada ke nan shi kadai cikin fushi. “Me kuma wannan za ta gaya mini?”

A haka ya isa gida, ya girke motarsa a gurbin da yake ajiye ta a kofar gidansa, kafin da dare ya shigar da ita garejinsa. Koda ya tsaya da motar, ya dauki kimanin minti 15 bai fito ba, ya ci gaba da kai-komo da tunani iri-iri. Ya lura cewa tun bayan sulhun da yayarsa ta yi musu, shi da uwargidansa Farida, bai kara samun sukunin kula budurwarsa Saratu ba, tsawon mako biyu ke nan. Koda ya yi tafiya Dubai domin sayo haja, har ya dawo bai sanya ta cikin lissafi ba. Bayan ya dawo ne yaron shagonsa ya fada masa cewa Saratu ta zo a gigice tana nemansa amma bai kula da batunta ba.

Ba ya kiranta a waya kuma ita kanta ba ta kira shi ba tunda ya dawo. A duk lokacin da ya kudiri aniyar zuwa wajen Saratu, sai zuciyarsa ta nuna rashin kaunar haka. Yanzu kuma da kawarta ta kira shi, sai wani bakin ciki ya bijiro masa, ya kashe wayar ma gaba daya. Shi kansa bai san dalilin da ya sanya haka ke faruwa da shi ba, kuma ya nemi laifin da Saratu ta yi masa wanda ke tunzura shi har yake juya mata baya haka, amma ya rasa.

“Shin wai wane laifi ma wannan yarinyar ta yi mini ne?” Alhaji Baba ya kara nutso cikin tunani, a yayin da ya kara jingina bayansa a kujerar mota, hannunsa daya a kan sitiyari.

“Tun lokacin da muka yi sabani da Farida, har ta kai ga yin yaji ban samu wani sukuni ba, musamman dangantakata da Saratu.” Ya ci gaba da zancen zuci. Ya zuwa yanzu dai, ya shafe kusan minti biyar a cikin mota, tun bayan tsayawarsa a kofar gida.

“Saratu dai ina kaunarta kuma tunda farko na sanya wa zuciyata niyyar aurenta. A dan bincikena… kodayake a gaskiya ban yi wani bincike kanta ba, al’amura suka fara jagwale mana sanadiyyar matsalar da Uwargida Farida ta bijiro mana da ita. Wai ni ne har da zuwa biko… uhmm, ai wannan ma bai kamata in kira shi yaji ba. Idan ba haka ba, yaushe matarka za ta ce ta yi yaji kuma ta tafi gidan yayarka ta zauna?”

“Koma dai me ke nan, wannan alama ce ta kauna.” Ya saki wani murmushi, har hakoransa suka bayyana. “Hakika akwai kauna mai girma da mutuntawa tsakaninmu, tun lokacin da muka yi aure har zuwa wannan rana. To me ya sanya Farida take neman canjawa a lokaci daya?”

Ya shaki wani gwauron numfashi, ya nisa. “Farida tana neman canja ra’ayi saboda zan mata kishiya. Ta taba gaya mini cewa ba ta kaunar kishiya. To amma haka ya kamata rayuwa ta kasance? Ni dai ba kiyayya ce za ta sanya in kara aure ba kuma ban ce zan wulakanta Farida ba, to me zai sanya ta sanya mini karan-tsana saboda zan kara aure? Allah Ya hore mini dukiya daidai gwargwado. Ina da sana’a mai karfi, ina da cikakkar lafiya, ina da… ina da….”

Ya sanya hannu ya bude kofar mota da niyyar fitowa. Ya mika hannu ya dauko wata karamar jaka da ke ajiye a kujerar baya. Har ya sako kafa daya waje da niyyar fitowa daga motar, sai kuma ya dawo ya sake zama. Kafarsa ta hagu na waje, daya kuma tana cikin mota. A haka ya ci gaba da zama kuma ya ci gaba da jerangiya da tunanin zuci.

“Shin ko Farida ta fara bin malaman tsibbu ne?” Ya bijiro da wani zargi amma kafin ya natsu da wannan sai wata zuciyar ta yi sauri ta karyata wannan batu.

 

Za mu ci gaba

 

 

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

 

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili! Ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Bayan haka, ina shaida muku cewa daga makon gobe, FDK zai tafi hutu na wata guda cur, don haka wannan fili naku mai albarka shi ma zai tafi hutu. Amma kada ku damu, da zarar hutun ya kare, insha Allahu za mu dawo da shirye-shirye masu kayatarwa. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 

Dahiru Sunusi Mangal Abuja (08039500115):

Assalamu alaikum, wannan labari yana yi wa mata hannunka mai sanda ne. Duk dadewar da mace za ta yi a gida, idan ta kai zuciya nesa Allah zai fito mata da mijin aure. Wallahi da ki auri sha-ka-tafi, gara ki yi jinkiri a gida har na kwarai ya fito! Sannan duk wanda ya fito yana sonki, kafin ki ba shi izini ya fito, ki tabbatar kin yi Sallar Istikhara, domin neman zabin Allah.

 

Daga Uwargidan B.Z. Kauran Namoda:

FDK, barka da kokari, ina mika gaisuwata ga ma’abota wannan shafi. Ni tsohuwar mai bibiyar wannan shafi ne amma sabuwar mai sharhi ce. Na rubuto ne kawai domin in mika gaisuwata a wurin uwargida a gidan Alhaji Baba. Ina miki jinjinar ban-girma a kan namijin kokarin da kike yi wurin bibiyar al’amuran maigidanki, don dorewar zaman lafiyar gidanki. Haka ake son duk wata uwargida ta zama.

 

Daga Sakinat Ahmad Utako-Abuja (09091677786):

Sallama irin ta addinin Musulunci, gaskiya muna jin dadin karanta Aminiya. Sako na musamman ga ma’aikatan jaridar Aminiya da masoyana. Har yanzu ina bayan Saratu Sarauniyar Mata, domin shiriya na wurin Ubangiji. Allah Ya ba mu maza masu adalci, amin.

 

Daga Abdulrahaman Isah Kiyawa:

FDK, da fatar kana lafiya da duk dan wannan fili, amin.

 

Daga Garkuwan FDK Mahmud M. Rabi’u Fatakwal (08140645275):

FDK, ina yi maka fatar alheri, yaya kokari? Allah Ya kara basira da daukaka, amin. Don Allah a isar mini da gaisuwata zuwa abar kaunata Zainab Ummi ’yar mutanen Kofar Waika Kano.

 

Daga K.S.K. Pandogari (09075112894)

Ya ku ma’abuta shafin FDK! Da fatar kun tashi lafiya. Bayan gaisuwa da fatar alheri, so mai hana sukuni, so sinadarin zuci, so abin farin cikin zuciya, so ginshikin rayuwa. A kullum burin masoyan gaskiya, shi ne aure, soyayyar da aka gina ta kan gaskiya babu yaudara. Allah Ya kara mana son gaskiya, amin.

 

Daga Sulaiman Tambai  08167090442:

FDK, Allah Ya kara basira. Yau wata biyu ina bibiyar wannan shafi, ni ina bayan Uwargida Farida. Wannan ya zama darasi ga wanda ba ya daukar shawara.

 

Daga Halimatu Yusif Katsina:

Hakika muna jin dadin kasancewa tare da wannan labari. Duk mako ina jin dadin kasancewa da shi, Allah Ya kara basira.

 

Daga Asiya Mukhtar (09032763124):

FDK, ina maka fatar Alheri. Gaskiya ina goyon bayan Uwargida Farida, ina yi wa kowa da kowa fatar alheri, na gode.

 

Sa’adiyya Maikaka Funtuwa:

Assalamu alaikum ma’abuta karatun jaridar Aminiya, musamman masu bibiyar shafin FDK mai dogon tarihi; ina mika gaisuwa gare ku.

 

Daga A’isha Ibrahim Jajere (07039578743):

Assalamu alaikum FDK, Allah Ya sa albarka ga dimbin masoya wannan fili. Ina masu goyon bayan Saratu? Amma ni ina bayan Uwargida Farida. Ina mika sakon gaisuwa ga iyayena da dan uwana.