✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiga-jigan tsohuwar jami’yyar CPC na son Malami ya zama abokin takarar Tinubu

Tinubu zai gana da Buhari a ranar Laraba.

Wasu jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar CPC na son jam’iyyar APC ta zabi Ministan Shari’a, Abubakar Malami a matsayin wanda zai yi wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu mataimaki.

Wannan dai na zuwa ne yayin da wa’adin da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta debar wa jam’iyyu domin mika mata sunayen ’yan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, inda jam’iyyun ke ci gaba da fadi-tashi domin ganin cewa ba su yi zaben tumun dare ba.

Hukumar INEC dai ta ce duk jam’iyyar da ba ta mika sunan abokin takarar masu neman kujerar Shugaban Kasa ba zuwa ranar 17 ga watan Yuni, to za a hana ta shiga Babban Zaben na badi.

Aminiya ta ruwaito cewa jam’iyyar APC da PDP sun takaice zabin abokan takararsu zuwa wasu manyan ‘yan siyasa.

Wata majiya mai tushe ta ce bangaren dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu ya takaice a kan Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, yayin da kuma magoya bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, sun kammala tattaunawa kan a tsayar da gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matasayin abokin takarsa.

Sai dai kuma wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar CPC wadda tana cikin jam’iyyun da suka zama tsintsiya madauri daya aka samar da jam’iyyar APC, na shirin tuntubar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya ba da shawarar a tsayar da Ministan Shari’ar wato Malami, ko kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

“Wasu jigajigan tsohuwar jam’iyyar CPC na shirin tunkarar Shugaba Buhari domin ya amince a tsayar da Abubakar Malami ko Hadi Sirika a matsayin abokin takarar Tinubu a Zaben 2023,

“Amma akwai yiyuwar shugaban kasar zai maimaita abin da ya yi gabanin Babban Taron jam’iyyar APC; zai bayar da kunnuwan sauraro ga kowa da kowa amma tabbas zai bar dan takarar [Tinubu] ya fadi ra’ayin wanda yake so ya yi aiki tare.

“Za su hada kai wajen fitar da dan takarar da ya dace wanda zai kawo kuri’a da karbuwa domin babbar manufa ita ce APC ta ci gaba da rike mulkin kasar,” inji majiyar.

Bayanai sun ce an shirya ganawa tsakanin Tinubu da Shugaba Buhari a ranar Laraba, kuma batun abokin takarar na cikin muhimman abubuwan da za su tattauna.

Masu fashin-baki kan al’amuran siyasa na ganin cewa zaben abokanan takarar ne zai taka rawar gani wajen tabbatar da nasara ko akasin haka a zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.