✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar da yara miliyan biyu ba sa zuwa makaranta

Yara kimanin miliyan biyu ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara, daga cikin yara fiye da miliyan 10 marasa halartar makaranta a Najeriya. Hakan…

Yara kimanin miliyan biyu ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara, daga cikin yara fiye da miliyan 10 marasa halartar makaranta a Najeriya.

Hakan ta sa gwamnatin jihar bullo da shirin sanya ilimin boko a tsarin makarantun allo da kuma ciyar da almajirai a makarantun.

Manufar shirin ita ce, ”Ba wa wadannan yara damar lakantar ilimin dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace”, a cewar hukumar ilimin bai daya ta jihar.

Shugaban hukumar Abubakar Aliyu Maradun ya kara da cewa za a fara shirin ne yara 30,000 a makarantu 280 daga a kananan hukumomi takwas.

Ya ce ”An tanadi kayayyakin karatu, littattafan yara da kuma malaman, sannan muna ba su abinci sau daya a kullum”.

Jihar ta gano girmar matsalar yaran marasa zuwa makaranta ne bayan alkaluman da a baya suka nuna cewa yara miliyan daya ne a jihar ba sa zuwa makaranta.

Zamfara na daga jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari, sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Ayyukan bindiga a jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama baya ga tilasta wa dubbai tserewa daga gidajensu.