✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Gombe za ta fafata a gasar nakasassu ta kasa ta farko

Gasar dai ita ce irinta ta farko da za a gudanar a matakin kasa

Jihar Gombe ta shiga jerin jihohin da za su fafata a wasannin gasar nakasassu ta kasa irinta ta farko a matakin kasa da za a gudanar a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Jihar ta ce za a fafata da ita a dukkan nau’i shida na gasar.

Da yake yi wa ’yan wasan jawabi kafin su bar Gombe, Shugaban Hukumar wasanni ta jihar, Mista Olanre Daniel, gargadin su ya yi da cewa su zama jakadu na gari masu kiyaye dokokin da aka shimfida musu yayin gasar.

Shugaban ya kuma gode wa Gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa amincewa da ba su dama su shiga a fafata da su a gasar.

Ya kuma gargadi ’yan wasan da cewa ba kallon gari za su je ba, za su je ne don ciyo wa Jihar azurfa da tagulla.

Olanre, ya tabbatar wa da ’yan wasan cewa suna da goyon bayan gwamnati har a kammala gasar.

Wasannin da za su shiga a fafata da su din sun hada da kwallon guragu, da kwallon nakasassu da na kurame da na masu daga karfe da wasan tsere na guragu da dai sauransu.