✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Kano na neman kaso na musamman daga lalitar Tarayya

Gwamnatin Kano na neman a sake tsarin rabon kudade tsakanin jihohi da Gwamnatin Tarayya.

Jihar Kano ta bukaci a rika ware mata kaso na musamman idan aka tashi rabon kudaden shigar Gwamnatin Tarayya, wanda take neman a sauya tsarin rabawa tsakanin jihohi da Gwanatin Tarayya.

Gwamnatin Jihar Kano ce ta mika bukatar ganin ana ba wa jihar karin kashi daya cikin 100 idan aka tashi rabon kudaden Gwamnatin Tarayya ne saboda muhimmancin matsayinta a Najeriya.

Ta gabatar da bukatar hakan ne a taron sauraron ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Gabas da Hukumar Rabon Kudaden Tarayya ta gudanar a Kaduna ranar Litinin.

Da yake gabatar da bukatar, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, kuma shugaban ayarin da ya wakilici jihar (SSG), Alhaji Usman Alhaji, ya ce gwamnatin jihar ta cancanci karin kaso na musamman, idan aka yi la’akari da karin nauyin da ke karuwa kanta, sakamakon kwararowar ’yan gudun hijira daga jihohin Katsina, Zamfara, Kebbi, Sakkwato da sauransu da matsalar tsaro ta addaba.

Alhaji Alhaji ya ce baya ga zamanta babbar cibiyar kasuwanci, Kano ita ce jihar da fi yawan al’umma a Najeriya, inda ta tattaro mutane daga kowane bangare.

A don haka ya roki Gwamnatin Tarayya ta amsa rokon, domin taimaka wa ci gaban gabangaren kasuwanci da noma da masana’antu a jihar “wanda zai yi tasiri matuka wajen kowar karuwar ci gaban kasa baki daya”.

Ya kuma koma da cewa tsarin rabon kudaden da ake amfani da shi a halin yanzu ya fifita Gwamantin Tarayya a kan jihohi da kananan hukumomi, wanda ya ce ba adalci ba ne.

Ya ba da shawarar a sauya tsarin rabon kudaden ta yadda a cikin kashi 100 Gwamnatin Tarayya za ta dauki kashi 41, jihohi kashi 34, kananan hukumomi kashi 24, sai kashi 13 na jihohi masu arzikin mai.