✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jihar Katsina: Kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba

A can da in ana maganar siyasa, idan an zo Katsina sai dai a shafa Fatiha. Daga zamanin  sarakunan Habe, aka zo lokacin Jihadin Shehu Dan…

A can da in ana maganar siyasa, idan an zo Katsina sai dai a shafa Fatiha. Daga zamanin  sarakunan Habe, aka zo lokacin Jihadin Shehu Dan Fodiyo, Turawa mulki suka zo, Katsina ba kanwar lasa ba ce. Ta fannin ilimi, kasuwanci balantana mulki. Can zamanin da, manyan malamai da yawa sun zo Katsina, sun zauna. Lokacin da Musulunci ya zo Katsina a karni na 15, zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Korau, wanda ya kasance Sarki Musulmi na farko a lokacin Katsina ta kasance cibiyar ilimi da addinin Musulunci. A wancan zamanin ne aka gina Hasumiyar Gobarau, wadda take dadai da jami’a irin ta yanzu. Ita dai wannan hasumiya ta kasance masallaci sannan kuma cibiyar koyon ilimin addinin Musulunci.  A  wancan zamanin ne aka yi waliyyan da Katsina ke takama da su yanzu, kamar Waliyi Jodoma wanda shi ne mahaifin Waliyi Dan Marina.

Lokacin da Turawa suka ci Daular Usmaniyya da yaki,  Katsina ta samu ci gaba a wancan zamani, ta bangaren ilimin boko an kafa kwalejin nan mai tarihi wadda ita ce ta yaye akasarin shugabannin farko na Arewa irin su Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardauna da Sa Abubakar Tafawa Balewa, Firayi Ministan Najeriya na farko da Sa Kashim Ibrahim da Aliyu Makaman Bida da sauransu. Masana tarihi na danganta ci gaban da Katsina ta samu zamanin Turawa a kan kwarewa ta shugabanninta musamman Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, wanda yanzu ake wa Katsina kirari da sunansa, wato “Ta Dikko Dakin Kara.”

Haka aka yi ta gangarowa, albarkar shugabannin farko na bibiyar Katsinawa. To sai dai yanzu tarihi na neman juya wa jihar baya, saboda rauni na shugabanni da ake samu. Dama idan Allah Ya yi wa mutum baiwa, kuma ya ki amfani da baiwar, sai ta subuce, a koma ana cizon hannu.

A yanzu maganar da ake, iskar nan mai juyawa, Katsina ba ta da wani zakara wanda za a iya kwatanta shi da marigayi Janar  Hassan  Usman ko marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa, kai ko kamar marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa babu.

Me ya sa? Saboda wadanda yanzu ke jagorancin jihar, na yaye ’yan barandar siyasa suna aika su majalisun tarayya ana mana dariya. Wai wadannan su ne za su wakilci jiha kamar Katsina. Wadanda kuma ke ganin su ’yan boko ne ba su da wani amfani. Ba su da taimakon komai, daga su sai matansu da ’ya’yansu da karuwai da ’yan daudu. Za ka ji an ce ai wane ya rike mukami kaza, amma almajirin gidansa mai sawo musu cefane sai ka raina su, saboda bakin ciki da keta.

Siyasar Katsina wadansu ’yan tsirarri ne ke juya ta. Wadannan ’yan tsirarri sai abin da suka ga dama suke yi. Su ake ba kwangila, yaransu ake nadawa a mukamai.

Wani abu da zai kara dakushe siyasar Jihar Katsina shi ne, wulakanta matasa da daukarsu ba a bakin komai ba. Mu kuwa mun san wadannan matasan da koyaushe ake kyama, ko an ki, ko an so, wata rana su ne shugabannin Katsinawan komai bakin cikin mutum. A baki dayan matasan jihar, ba ka da wani zakara, saboda siyasar banza ta kyashi da bakin ciki da zari da ake yi a jihar.

Duk kwakwalwarka, duk kokarinka, duk kwarewar matashi in dai a Katsina yake, to in dai ba dan kowa ba ne, kuma ba boyi-boyin wani kasurgumin azzalumi mai mulki ba ne, to sai dai ya kare yana bata kwakwalwarsa da basirarsa saboda bai da daraja bai da mutunci a idon shugabannin.

Yau muna karni na 21, amma babu wani tanadi da masu kiran kansu shugabanni suka yi wa matasan Jihar Katsina. Wannan ya sa sai dai mutum ya tafi wata jihar ci-rani, in ba haka ba kuwa to zai wulakanta, ya tozarta.

Ba za a rasa ’yan kalilan na kirki ba, amma marasa kirki da tausayi, sun fi yawa a jihar, kuma a ra’ayina wannan zai sauya tarihin da aka san Jihar Katsina da shi nan gaba kadan. Ai Hausawa na cewa abin da ka shuka shi za ka girba. To za mu girbi abin da muka shuka a Katsina.

Katsina za ta iya dawo da tagomashinta, idan shugabannin jihar suka taimaki matasan jihar. Ba dole sai dan banga ko dan barandar siyasa ba, ba dole sai dan jam’iyya ba, ko wani bara-gurbi. In dai mutum Bakatsine ne, to a taimaka masa. Wadanda ba su da aiki a samo musu aiki na Gwamnatin Tarayya,  karamar hukuma da jiha da ma kamfanoni masu zaman kansu. Wadanda ke son karatu a taimake su su yi karatu daga nan har zuwa birnin Sin. Wadanda ke son kasuwanci a taimake su da jari da samar musu kasuwa ko’ina a duniya. Wadanda ke da wata basira ta waka ko fim ko rubutu ko kere-kere a taimaka masu. Wannan shi ne abin da ya kamata a ce ana yi wa matasa idan har ana son gani ci gabansu da kuma ci gaban Jihar Katsina da Najeriya baki daya.

 

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina

Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa 08165270879