✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Kebbi ta tura dalibai 117 kasar waje karatun Aikin Likita da Injiniya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tura dalibanta 117 zuwa kasar waje domin su yi karatun aikin likita da kuma aikin injiniya.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tura dalibanta 117 zuwa kasar waje domin su yi karatun aikin likita da kuma aikin injiniya.

Tuni daliban da aka dauki nauyin nasu suka bar Najeriya zuwa kasashen Ukraine, Indiya da kuma Sudan inda za su yi karatun nasu a fannonin aikin likita da kuma injiniya.

Karon farko ke nan da gwamnatin jihar ta dauki nauyin dalibanta su yi karatu a kasashen ketare, a cewar Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Da yake bankwana da daliban, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta tura daliban zuwa kasar waje su yi karatu ne domin su zama wakilanta a idon duniya, amma ba wai don babu jami’o’i masu inganci ba a Neriya.

“Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya nuna mana wannan rana da ’ya’yanmu za su je su yi gogayya da takwarorinsu daga sauran sassan duniya a harkar neman ilimi.

“Mun san muna fama da matsaloli, amma ilimi yana daga cikin abubuwan da muka fi ba wa muhimmanci, ciki kuwa har da tura ’ya’yanmu zuwa kasar waje domin su samo ilimi.”

Da yake jawabi, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Kebbi, Farfesa Muktar Bunza, ya ce tuni Gwamna Bagudu ya fitar da Dala miliyan daya da dubu sittin domin biya wa daliban kudin makaranta, wurin kwana, kudin abinci da na kashewa.

“An kuma kashe Naira miliyan 355 wurin biyan kudin tafiye-tafiye, kudin bisa, da tantancewa da kuma gwaje-gwajen lafiya da ake bukata domin tafiyar daliban su 262.”