✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Yobe ta yi sabon Kwamishinan ’Yan Sanda

Haruna dai shi ne zai kasance wanda ya rike mukamin na 31 tun bayan kirkiro Jihar.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da sashen binciken sirri, wato CID a hedkwatar rundunar da ke Jihar Yobe, Haruna Garba, ya zama sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar.

Haruna dai shi ne zai kasance wanda ya rike mukamin na 31 tun bayan kirkiro Jihar

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannu Kakakin rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, a Damaturu ranar Talata.

Nadin nasa ya biyo bayan samun karin girman da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Yahaya Sahabo Abubakar, ya yi zuwa Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan Sanda na kasa (AIG).

Sabon Kwamishinan dai, wanda dan asalin Jihar Kogi ne da ya kammala digirinsa a bangaren Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Maiduguri, sannan ya samu digiri na biyu a harkar Huldar ta Kasa da Kasa daga Jami’ar Uyo dake jihar Akwa Ibom.

 

Sanarwar hakan tana dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sanda mai helkwata a garin Damaturu ASP Dungus Abdulkarim.

CP Garba, ya fara aikin Dan sanda ne a matsayin ASP a ranar 3 ga watan Maris din shekarar 1990, inda ya samu horo a harkar kula da dabarun mulki.

CP Haruna ya kuma rike wannan mukami a bangarori daban-daban na rundunar a fadin kasar nan.