✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin da za a yi gumurzu a zaben gwamnoni

An fi ganin batun rikici a zaben saboda kasancewarsa kusa da talakawa kuma kar ta san kar.

A gobe Asabar 18 ga Maris ne za a fafata zaben gwamnoni da majalisun dokoki na jihohi bayan Hukumar INEC ta dage zaben da mako daya.

Aminiya ta ruwaito yadda zaben zai zo daban kasancewar sakamakon zaben Shugaban Kasa da majalisun tarayya sun zo da ba-zata a wasu jihohin, wanda hakan ya sa lissafin siyasar ya canja.

Bayan sake salon a neman kuri’a da lallama, Aminiya ta gano wasu jihohi da take ganin zaben na gobe zai fi zafi, wanda hakan ya sa ake cikin fargaba a jihohin.

Sakamakon sabani da takaddamar kafin zabe da a wani lokaci ke hade da rikici a tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihohin, ana jin tsoron abin da ka iya biyowa baya.

Mutanen wadannan jihohi musamman magoya bayan manyan ’yan takara na cike da fargabar barkewar rikici, bisa ga irin abubuwan da suka biyo bayan zaben Shugaban Kasa da aka gudanar.

Aminiya ta gano jihohin da za a fi gumurzu a zaben na gobe sun hada da Kaduna da Zamfara da Legas da Kano da Gombe da Ribas da kuma Bauchi inda aka yi ta a kiraye-kiraye ga jami’an tsaro su tsaurara matakan tsaro a jihohin kafin gudanar da zaben.

Jihar Kano

A Jihar Kano, mazauna jihar na fargabar maimaita abin da ya faru a zaben Shugaban Kasa da ya gabata a wasu kananan hukumomi da kuma tsoron barkewar irin rikicin da ya faru a bayan zaben gwamnoni a shekarar 2019 a jihar.

Rundunar ’Yan sandan Jihar ma ta tabbatar da shirin yin amfani da ’yan daba da wasu ’yan siyasa ke son yi don bata zaben.

Za a iya cewa zaben na Gwamna a jihar abu ne da zai iya zama ma na a-mutu-ko-a-yi-rai a tsakanin manyan jam’iyyu biyu da ke adawa da juna, inda Jam’iyyar APC ke ganin ita ce wacce ludayinta ke kan dawo don haka dole ta ci gaba da damawa a jihar ana sha, yayin da Jam’iyyar NNPP take ganin karanta ya kai tsaiko, don haka lokaci ya yi da za ta karbe mulki daga APC.

A wani gefe kuma abin da ya faru a zaben shekarar 2019 yana nan daram a zuciyar manyan jam’iyyun wato batun “inconclusive” inda Hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

A bangaren jam’iyya mai mulki duba da cewa hakan da aka yi a 2019 ya janyo musu samun nasara don haka a yanzu suke ganin ko hakan aka yi, su daidai ne.

Sai kuma a bangaren Jam’iyyar NNPP duba da cewa lamarin ya janyo musu faduwa duk da cewa suna ganin nasara a fili kasancewar su ke da kuri’u mafi rinjaye, a wannan lokaci za su yi tsayuwar daka wajen kauce wa abubuwan da suka janyo faruwar hakan don ganin tarihi bai maimaita kansa ba.

Sai dai idan aka dubi rikicin gida da ke faruwa a Jam’iyyar APC za a iya cewa idan ta yi wasa, hakan na iya ba Jam’iyyar NNPP nasara a jihar.

Kowa na sane da yadda Jam’iyyar APC ko a ce Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya zabo tare da tsayar da dan takarar Gwamna wato Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna daga cikin dimbin maso son gadar kujerar tasa; ciki kuwa har da zababben Sanatan Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin wanda ya dade yana zawarcin kujerar tare da yi wa Gwamann biyayya da hidima don ganin ya tsayar da shi a matsayin magajinsa.

An ce wannan abu da Gwama Ganduje ya yi ya fusata ran Sanata Barau duk da rarrashi tare da yarje masa da Gwamanan ya yi a kan ya ci gaba da rike kujerarsa ta Sanata.

A gefe guda akwai dadaddiyar hamayya a tsakanin Sanata Barau da dan takarar Mataimakin Gwamnan, Alhaji Murtala Sule Garo wadanda dukkansu suka fito daga Kano ta Arewa.

Har ta kai a duk lokacin da aka hadu da Garo da Barau a wuri daya, sai an yi rigima a tsakanin yaransu.

Wannan lamari ya janyo ana hasashen cewa bangaren Sanata Barau wanda a yanzu ya sake lashe kujerarsa za su iya yin zagon kasa su ki zabar ’yan takarar jam’iyyarsu tare da goya wa wasu jam’iyyun baya.

A wani gefen kuma akwai rikicin Alhaji Murtala Sule Garo da Shuagaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai Alhaji Alhassan Ado Doguwa wanda har ta kai a wani lokaci aka zargi Doguwa da fasa bakin Garo da kofin shayi yayin da wata rigima ta hada su.

Wannan ana ganin zai iya yin tasiri a zaben na Gwamna duk da cewa kotu ta hana Doguwa ziyartar mazabarsa a lokacin zaben Gwamna saboda tuhume-tuhumen da ake yi masa da suka danganci zabensa da yanzu haka suke gaban kotu.

Har ila yau ana ganin cewa ’yan takarar kujerun sanata da na Majalisar Wakilai da suka sha kaye a zaben 25 ga Fabrairu za su yi wa Jam’iyyar APC tawaye a wani tunani na “tunda mun rasa kowa ma ya rasa.”

Za a iya cewa akwai kanshin gaskiya a cikin wannan batu idan aka yi la’akari da yadda mafi yawansu suka tafi Abuja suka bar masu takara suna fama da yakin neman zabe su kadai.

Haka ana ganin mulkin da Jam’iyyar APC ke da shi a sama na Shugabancin Kasa ba zai yi wa jam’iyyar a jihar amfani ba, domin babu wani taimako ko goyon baya da za su sa ran su samu wajen cin zabe, duba da cewa akwai jikakkiya a tsakanin bangarrorin biyu.

Idan aka yi la’akari da irin bakaken maganganun da Gwamna Ganduje ya rika yi wa Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari inda ya yi zargin cewa Shugaban Kasar na yi wa Jam’iyyar APC zagon kasa a dalilin canjin kudin da ya yi.

A bangaren Jam’iyyar NNPP duk da cewa nata rikicin cikin-gidan bai shahara ba, domin su ma ’yan Kwankwasiyya na ainihi suna yi wa wadanda ba ’yan tsantsar ’yan Kwankwasiyya ba ko kuma wadanda suka zo daga wasu jam’iyyun kallon bare a cikin jam’iyyar.

Sai dai kuma an yi sa’a wannan ganin fifikon ba zai shafi zaben Gwamnan ba kasancewar dan takarar Gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam dukkansu ’yan ainihin Kwankwasiyya ne.

Wannan ya janyo za a iya cewa rikicin cikin-gida ba zai yi tasiri a takarar ba. Sai dai ana fargabar akwai wadanda suke son ’yan takararsu ne kawai a NNPP din, amma ba za su yi Abba Gida-Gida ba, wanda hakan ya sa ake fargabar rasa wasu kuri’u.

Kuma ana ganin dukkan ’yan takarar za su fuskanci matsalar karancin kuri’u idan aka yi la’akari da yadda mutane da dama suke bayyana cewa ba za su fita zaben ba sakamakon tsoron da suke yi na tashin fitina ko tarzoma a lokacin zaben.

A kwanan nan an ji yadda jam’iyyun suka jefi junanssu da cewa sun yi hayar ’yan daba daga wasu jihohin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya irin su Nijar da Chadi don su yi amfani da su wajen tayar da tarzoma a lokacin zaben na Gwamna.

Sauran jam’iyyun da suka hada da PDP da PRP da ADC da ADP da SDP da YPP da BP da YPP da APP sun gudanar da wani taron manema labarai inda suka yi korafin cewa suna da labarin yadda wasu jam’iyyu suka yi shirin yin magudi a zaben na Gwamna inda suka ce sun samu labarin cewa ’yan siyasar da suke zargi sun dinka yunifom na jami’an tsaro don rabawa ga mutanensu wadanda za su yi musu aiki inda suka yi kira ga Hukumar INEC ta sa ido a kan abin da ke faruwa tare da daukar matakin da ya dace.

Wasu mazauna jihar sun bayyana yadda magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP suka fafata a zaben Shugaban Kasa da ya gabata, inda suka ce rikicin da aka samu a kananan hukumomin Takai da Tudun Wada alama ce da ke nuna irin abin da ke shirin faruwa a zaben Gwamna duk da cewar Rundunar ’Yan sandan Jihar ta nuna wa kurciya baka inda ta sha alwshin kama ’yan dabar da suka nemi tayar da tarzoma a zaben da kuma za ta gurfanar da su gaban kotu tare da iyayen gidansu, amma duk da haka mutane na cikin dar-dar na rashin sanin abin da zai faru a lokacin zaben.

Jam’iyyar LP za ta iya lashe kujerar Fagge?

A zaben Shugaban Kasa a Kano babu Karamar Hukumar da Jam’iyyar ta LP samu kuri’un da ta samu a Fagge, ana danganta nasarar tata da irin ruwan kuri’un da kabilu da kuma Kiristoci suka yi wa jam’iyyar duba da cewa ita ce jam’iyyar da akasarin Kiristocin Najeriya suka zaba tun daga kan ’yan majalisa da sanatoci har zuwa kan kujerar Shugaban Kasa.

Idan aka duba Jam’iyyar LP ta samu kuri’u mafiya rinjaye a mazabun Sabon Gari West da East yankunan da Kiristoci suke zaune a birnin jihar baya ga dimbin kuri’un da jam’iyyar ta samu daga mazabar da dan takarar jam’iyyar Shu’aibu Habungyare ya fito wato Fagge D.

Duk da cewar Baturen Zaben yankin Farfesa Shehu Usman bai sanar da ainihin kuri’un da kowace jam’iyya ta samu ba, sai dai daga sakamakon da aka fara tattarawa a cibiyar tattara zabe na Karamar Hukumar Fagge al’umma sun ce dan takarar Jam’iyyar NNPP Barista M.B Shehu ne kan gaba sannan dan takarar Jam’iyyar LP, Shu’aibu Habungayare ke biye masa sai kuma dan takarar Jam’iyyar APC wato Kwamared Sulaiman Goro.

A yanzu haka da ake jiran Hukumar INEC ta sanar da lokacin da za ta sake zabe a wasu mazabun da ta soke a Karamar Hukumar Fagge, mafiya yawan ’ya’yan Jam’iyyar APC a yankin sun sha alwashin idan har suka ga ba za su iya kaiwa ga nasara ba duba da cewa su ne a matsayi na uku, to za su goya wa dan takarar Jam’iyyar LP baya inda za su hadu su kwada Jam’iyyar NNPP da kasa.

Wannan ya sa ake tunanin LP za ta iya samun nasara a zaben majalisar jiha a yankin.

Jihar Legas

Jihar Legas daya ce daga irin jihohin da ke fuskantar barazana a zaben gobe Asabar kamar yadda mazauna jihar suka bayyana saboda yadda ’yan daba suka ja daga.

Shan kayen da Jam’iyyar APC ta yi a jihar a zaben Shugaban Kasa, jam’iyyar mai mulki ke son dawo da karfinta don kwato jihar da ta dade tana mulka a fiye da shekara 20.

Hankali ya yi matukar tashi da harin bindigar da aka kai wa dan takarar Gwamnan jihar karkashin Jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour a garin Epe.

Sai dai Rundunar ’Yan sandan Jihar ta ce ta dauki matakan da za ta dakile tashin duk wata fitina a sassan jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Idowu Owohunwa ya umarci dukkan shugabannin ’yan sandan yanki da DPO-DPO su tashi tsaye wajen bayar da kariya a tashoshin zabe da ke yankunansu da sa ido tare da lura da duk wuraren da ke da barazana don daukar matakan tsaro a wuraren a lokuta da kuma bayan zaben.

Masana da masu fashin bakin siyasa na hasashen za a yi gumurzu sossai a zaben Gwamna a Jihar Legas.

Masanan na ganin za a iya gwabzawa a tsakanin Jam’iyyar APC da manyan masu kalubalantarta wato PDP da LP, musamman ganin yadda LP ta ba da mamaki a zaben Shugaban Kasa.

Akwai masanan da ke hasashen cewa Jam’iyyar LP a Legas, za ta iya hadewa da PDP domin ta kawar da gwamnatin APC a jihar.

Jihar Zamfara

Mazauna Jihar Zamfara ma suna bayyana fargabar da suke da ita ta barkewar rikici a yayin zaben na gobe Asabar.

Hatta ’yan takarar na jefa tuhume-tuhume da sukar juna kan hare-haren da yawanci magoya bayansu ke kaiwa.

Manyan ’yan takarar su ne Gwamna Bello Mohammed Matawalle, wanda ke neman zarcewa a karkashin Jam’iyyar APC da abokin takararsa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Dauda Lawal Dare.

Tun bayan fara kamfen ne ake samun hare-hare a tsakanin magoya baya da ofisoshinsu da ababen hawa da allunan kamfen na ’yan takara a-kai-a-kai.

’Yan adawa a jihar na zargin hukumar yaki da daba ta jihar da musguna musu, zargin da hukumar ta musanta.

A jajibirin zaben da aka daga a makon jiya ne dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, Dokta Dauda Lawal Dare ya yi zargin an kai masa samame bayan harin da aka kai wa motar matarsa da hukumar ta yi.

Ya ce ayarin motocin matarsa na hanyar dawowa daga harkar jam’iyyarsu daga Gusau ’yan hukumar gwamnatin suka kai musu hari.

Wani dalilin fargabar kuma shi ne yadda yawancin masu kada kuri’a ba su samu damar kadawa ba saboda tsoron harin ’yan bindiga da aka tsoratar da su a kai.

Jihar Bauchi

A Jihar Bauchi kuwa, akwai fargabar yamutsa hazo a tsakanin magoya bayan Gwamna Bala Mohammed (Kauran Bauchi) na Jam’iyyar PDP da na Iya Mashal Sadikue Baba Abubakar na APC.

A watan jiya jam’iyyun PDP da APC suka rike wa juna wuya kan arangamar da ta kai ga kashe mutum uku da jikkata wasu da dama daga magoya baya a yayin gudanar da kamfe.

Wannan lamarin ya jefa tsoro a zukatan mazauna jihar inda wasu suka bayyana yadda rayuwarsu ke cikin hadari a zaben Gwamna da ’yan majalisar jihar.

Tsoron nasu ya dada tabbata ne ganin yadda manyan ’yan takarar ke yawon kamfen da gaggan ’yan dabar siyasa da sunan kungiyar mafarauta inda suke rike da makamai a lokutan yawon kamfen don razana abokan adawarsu.

Ra’ayoyin jama’a sun bambanta kan sabon angon da Jihar Bauchi za ta yi, yayin da wasu ke ganin manyan jam’iyyu na APC ko PDP ne za su lashe zaben, wasu na gani dan takarar Jam’iyyar NNPP na iya rabagardama.

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya dogara ne da irin ayyukan raya kasa da ya yi, musamman gina hanyoyi da asibitoci da gyaran makarantu da gina gidajen hakimai da samar musu da ababen hawa da sauransu.

Sai dai duk da kokarin da wasu ke ganin Gwamnan da mukarrabansa sun yi, wasu na ganin ya gaza a wasu muhimman abubuwan inda suke zargin cewa yana tafiye ne kawai da danginsa da abokansa a gwamnatin.

Shi kuwa Iya Mashal Sadikue Abubakar na Jam’iyyar APC, yana da magoya baya sosai, sannan a zaben da ya gabata mako uku da suka gabata, APC ta kawo Sanata daya daga cikin uku, kuma ta samu nasarar kawo ’yan Majalisar Wakilai biyar cikin 12.

Haka yana tare da gogaggun ’yan siyasa irin su tsohon Gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da Sanata Nazeef Gamawa da sauransu kuma a duk lokacin da y a fita kamfe, ana ganin yadda dimbin magoya ke tarbarsa a dukkan kananan hukumomin jihar 20.

Jihar Sakkwato

A Jihar Sakkwato ma akwai barazanar aukuwar rikici a tsakanin mazauna jihar a lokacin zaben Gwamnan saboda irin kalaman da shugabannin siyasa ke furtawa da hankulan mutanen jihar ke dada tashi a sanadiyyar furucinsu.

Aminiya ta ruwaito yadda rikici ya kai ga soke wasu akwatunan zabe sama da 400 abin da ya sa har zuwa yau Hukumar INEC ba ta bayyana sakamakon ba.

An ce ’yan takara da jam’iyyunsu sun yi amfani da ’yan daba wajen yamutsa zaben a wuraren da suke ganin ba za su ci zabe ba, wanda hakan ya kai ga hukumar ta soke wadannan akwatunan da rumfunan zaben gaba daya.

An kuma samu rahoton yadda ’yan bangar siyasa suka lalata kuri’u da akwatunan zabe a wasu wurare, abin da ya sa wasu suka ce ba za su fito don kada kuri’a a gobe ba.

Jihar Gombe

Mazauna Jihar Gombe ma na daga cikin masu fargabar samun hatsaniya saboda harkar Kalare kamar yadda aka samu a wasu sassan jihar a zaben da ya gabata.

Kafin zaben 25 ga Fabrairu na Shugaban Kasa, an samu rahoton jikkata mutum biyar da ’yan Kalaren suka yi lokacin da suka kai hari gidan wani fitaccen dan PDP a jihar, Alhaji Salisu Abdul’aziz. Abdul’aziz a baya yana Jam’iyyar APC ce kafin ya koma PDP.

Ya shirya tarurruka da kungiyoyin mata da matasa a gidansa da ke Jekadafari a tsakiyar garin Gombe lokacin da ’yan bangar siyasar suka kai masa hari don tarwatsa taron.

Masana harkar siyasar Gombe sun ce jam’iyya mai mulki kasancewar ta lashe zabe a sama, da kuma kasancewar tana rike da madafun iko, hakan zai iya ba ta nasara.

Sai dai magoya bayan PDP na ganin cewa alamomi sun nuna cewa su ne za su yi nasara a zaben na gobe duba da nasarar da suka samu a zaben mako uku da ya gabata Babban kalubalen da APC ke fuskanta shi ne rikicin cikin-gida a tsakanin mutanen Gwamna Inuwa da Sanata Goje, inda a yankin Goje ne kawai APC ta samu nasara a zaben mako uku da suka gabata, wanda hakan ya sa ake tunanin da wahala mutanen Sanata Goje su yi APC.

A daya bangaren kuma akwai Jam’iyyar NNPP da ake tunanin za ta iya tsintar dami a kala, sai dai ana tunanin duk da kokarin da dan takarar NNPP din Khamisu Mailantarki yake yi, aikin ya yi masa yawa kasancewar jam’iyyun APC da PDP sun yi karfi da yawa a jihar, wanda hakan ya sa ake tunanin daga cikin su biyun ne za a samu Gwamna.

Jihar Katsina

Tun bayan sanarwar dage zaben gwamnoni da majalisun jihohi, sai siyasar Jihar Katsina ta dauki sabon salon.

Jam’ iyyar APC mai mulki ta yi nasarar kama wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP musamman magoya bayan tsohon Gwamna Barista Ibrahim Shema wanda suka shiga takun-saka da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar ta PDP.

Ana haka kuma Daraktan Yakin Zaben Gwamna a APC Dokta Ahmed Dangiwa suka kira taron manema labarai inda suka yi zargin cewa, sun gano wani shiri da Jam’iyyar PDP ke yi na gayyato ’yan banga daga jihohin Kano da Zamfara domin kawo hargitsi a ranar zaben, zargin da PDP ta musanta ta bakin Daraktan Yakin Zaben Sanata Lado wato Dokta Mustafa Inuwa.

PDP cewa ta yi APC ce ke shirin yin magudin zabe wanda kuma suka sha alwashin cewa babu makawa sai sun bi duk hanyar da ta dace domin kare kuri’un da aka jefa musu.

Yayin da ake ta musayar maganganu a tsakanin manyan jam’iyyun biyu, kwatsam sai wata babbar baraka ta kunno kai a Jam’iyyar NNPP, inda dan takarar Mataimakin Gwamna Injiniya Muttaka Rabe Darma da Sanata Audu ’Yandoma da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Alhaji Sani Liti ’Yankwani da wasu manyan jam’iyyar ta NNPP suka kira taron ’ya’yan jam’iyyar a otel din Munaj da nufin yin mubaya’a ga dan takarar Gwamna na APC Dokta Dikko Radda wanda shi ma ya halarci taron.

Amma taron ba a gama shi lafiya ba sai da aka ba hammata iska a tsakanin magoya bayan dan takarar Gwamna na NNPP, Injiniya Nura Khalil da bangaren su Muttakan.

Hatta shi kansa Injiniya Nura sai da ya halarci wajen taron don gani da ido, inda kuma bangarensa suka yi zargin cewa su Muttaka sun yaudare su kuma suna kokarin sayar masu da jam’iyya ce ga APC.

Jihar Kaduna

A Jihar Kaduna ’yan takara shida ne sanannu ke neman su gaji Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i a ranar 29 ga Mayu lokacin da wa’adin mulkinsa zai kare.

’Yan takara kuwa sun hada da na Jam’iyyar PRP, Hayatudeen Lawal Makarfi wanda matashi ne. Sai Suleiman Othman Hunkuyi na Jam’iyyar NNPP wanda tsohon Sanata ne kuma tsohon Kwamishinan Kudi a jihar.

Sai dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki Sanata Uba Sani wanda Gwamnan Jihar ya zaba a matsayin wanda yake so ya gaje shi.

Sanata Uba Sani ya kasance Mai ba Gwamnan Jihar Shawara a Fannin Siyasa a shekara hudu na farko na Gwamna El-Rufa’i kafin ya zama Sanata a zaben shekarar 2019, inda yake wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

Akwai kuma Isa Ashiru Kudan dan takarar Jam’iyyar PDP, kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, sannan wannan ne karo na uku da yake takarar Gwamnan Jihar.

Akwai Jonathan Asake na Jam’iyyar Labour wanda shi ma tsohon dan Majalisar Wakilai ne kuma tsohon Shugaban Kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SUKAPU).

Akwai kuma surukin Shugaba Buhari wato tsohon dan Majalisar Wakilai Alhaji Sani Sha’aban na ADP.

Abubuwan da ake ganin za su ja hankali ko suke jan hankali a zaben shi ne yadda aka yi amfani da kabilanci da bangaranci da kuma addini a lokacin yakin neman zabe, wanda hakan ya jefa fargaba a zaukatan jama’a.

Akwai wadanda suka nuna rashin jin dadinsu ganin yadda malamai suka shiga cikin siyasar jihar dumu-dumu tare da nuna goyon bayansu ga jam’iyya mai mulki a jihar saboda takarar Musulmi da Musulmi, maimakon sauran ’yan takarar da suka dauki mataimaka Kiristoci.

Shigar malamai cikin siyasar ta sa wasu da ba sa ra’ayin hakan yin kalaman batanci ga malaman a kafafen sada zumunta.

Haka kuma Jam’iyyar PDP ta koka kan abin da ta ce na jami’an tsaro na kama mata magoya baya saboda siyasa.

A makon jiya an kama tsohon Kwamishinan Yada Labarai a Jihar Sa’idu Adamu wanda shi ne Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Kwamitin Yakin Zaben PDP.

Yadda za a magance afkuwar rikici — Kwararru da Kungiyoyi

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fage, ya ce an fi ganin batun rikici a zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi ne saboda kasancewarsa kusa da talakawa kuma kar ta san kar.

Game da yadda za a magance matsalar, Dokta Fagge ya ce dole ne ’yan siyasa su shiga taitayinsu tare da sanin me za su rika furtawa ko aikatawa domin su ne ke daukar nauyin ’yan jagaliyar siyasa.

“Suna daukar hakan kamar wani aiki ne ga masu kada kuri’a cewa duk inda ake da matsala to ba za a iya mulkarsu ba.

“Sannan ya kamata hukumar zabe ta rika daukar lamarin da muhimmanci ta yadda duk inda aka samu rikici to a yi bincike tare da hukunta duk wanda aka gano shi ne da laifi kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.

Ita ma kungiyar Sa Ido ta Transition Monitoring Group (TMG), ta ce akwai bukatar wayar dak kai da kuma daukar matakan da suka dace domin dakile rikicin zaben Gwamna da na majalisa a jiha.

Shugaban TMG, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce ana samun tsaftataccen zabe ne da ya gudana cikin nasara ta hanyar yadda hukumar ta gudanar da shi da kuma irin yadda dukkan masu ruwa-datsaki suka dauke shi.

“Wannan ne babban dalilin da ke kawo sa hannu a yarjejeniya na dukkan jam’iyyu da ’yan takararsu don a samu yin zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya a shekarar 2023.

“Wannan sa hannun da manyan masu fada-a-ji a kasa kan jagoranta a gaban duka masu ruwa-da-tsaki da suka hada da hukumomin tsaro da kungiyoyi da masu sa ido daga ciki da wajen Najeriya da kuma kafafen yada labarai,” in ji shi.

Ya ce dole ne gwamnati da masu ruwa-da-tsaki su tabbatar ’yan siyasa da jam’iyyunsu da magoya bayansu an gargade su kan illar tayar da rikici a lokacin zabe.

“A sa ido tare da jan layi ga duk wata kungiya ta daba da bangar siyasa domin su ne ’yan siyasa ke amfani da su wajen haifar da rikici,” in ji Rafsanjani.

Farfesa Oyesoji Aremu, wani kwararren masanin tsaro ya gargadi Rundunar ’Yan sandan Najeriya da kada ta daga wa wani dan siyasa kafa kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben gwamnoni da na majalisun dokoki na jihohi.

Aremu, wanda Farfesa ne a Jami’ar Ibadan, ya ce: ’yan sanda na bukatar kara kaimi wajen tattara bayanai da nuna kwarewa da bangare ne na matakin aikinsu.

“Ya kamata a wannan lokaci a tattara duk wata kwarewa tare da yin amfani da ita don sanin wane wuri ya kamata a kai dauki.

“Ina ganin ya kamata ’yan sanda su kira duk jagororin siyasa a jihohi su zauna da su duka. Tsarin da aka yi na sa hannu a dokar zaman lafiya a Abuja a kwafo shi a yi a kowace jiha a kuma gargadi ’yan siyasar tare da sanya musu ido a kai,” in ji shi.

Ba mu samu jin ta bakin Kakakin Hedikwatar ’Yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ba, lokacin da muka kira shi a waya bai amsa ba a daidai lokacin hada wannan rahoto, sai dai a baya ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Usman Baba ya gana da kwamishinonin ’yan sandan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja cewa an umarce su da su kasance cikin shiri tare da kasa kunnuwansu a ko’ina a ranar zabe.

A yanzu dai lokaci ne kadai zai raba wannan gardamar.