✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jini na kwarara a Najeriya – Sule Lamido

“Ko ma ya muka tsinci kanmu, zai zama tarihi. Amma yanzu dai tana kwararar jini.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sule Lamido ya koka kan tabarbarewar al’amuran tsaro a Najeriya inda ya ce ‘jini na kwarara a kasar’.

Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan wata ganawarsa ta sirri da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun ranar Lahadi.

A cewar wata sanarwa da kakakin Obasanjon, Kehinde Akinyemi, ya raba wa manema labarai a Abeokuta, ta ambato Lamido na cewa har yanzu tsohon Shugaban ya jaddada kwarin gwiwarsa kan Najeriya, duk kuwa da tarin kalubalen da ke fuskantarta.

Lamido ya ce, “Yadda za mu samu mu zauna lafiya yanzu shi ne babban kalubalen Najeriya, saboda yanzu babu wanda ya tsira.

“Ku duba fa wai har ma’aikatan gonar Baba [Obasanjo] ake sacewa a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa? Waye ya tsira kenan?” inji shi.

Tsohon Gwamnan ya ce ya je Jihar ta Ogun ne domin ya ziyarci Obasanjon a matsayinsa na uba kuma jagora, yana mai cewa ya same shi cikin karsashi da cikakkiyar lafiya.

Ya kuma ce, “Ya shaida min cewa yanzu tsufa ya cimmasa, amma na ce masa a’a, saboda har yanzu muna bukatarsa a kasar nan. Ya ce zai yi komai saboda Najeriya.

“Wannan abu ne mai karfafa gwiwa. Hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa nake son shi, kuma ya kara karfafa imanin da nake da shi akan Najeriya

“Mun tattauna batutuwa da dama da suka shafi Najeriya. A zahirin gaskiya, ko ma ya muka tsinci kanmu, wata rana zai zama tarihi. Amma a yanzu dai kam tana kwararar jini.